An kama shi yana bayan gida a masallaci a Kaduna
An kama dayansu yana bayan gida a masallaci saboda a ba shi N20,000
Dubun wasu mutane da suka hada baki dayansu ya yi bayan gida a masallaci rana tsaka a cikin watan Ramadan domin a ba shi kudi ta cika a Jihar Kaduna.
Wata kotun Musulunci a jihar ta ba da umarnin tsare mutum biyun da aka kama kan yin wannan aika-aika a harabar masallacin da ke layin Alkalawa a unguwar Tudun Wada da ke garin Kaduna.
- Ba mu hana yin tashe a Kano ba —’Yan sanda
- Matashiyar da ta yi karyar garkuwa da yi mata fyade ta shiga hannu
Dubun wadanda ake zargi ta cika ne har mutanen gari suka kama su bayan daya daga cikinsu ya yi bayan gida a masallacin da taimakon dayan abokin cin mushensa.
Bayan al’ummar unguwar sun cafke su ne suka mika su a hannun ’yan sanda kafin a gurfanar da su a gaban kotun ne kan zargin neman tayar da zaune tsaye.
Kotun da ke zamanta a Magajin Gari a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ta bayar da umarnin ne a ranar Alhamis.
Da yake jawabi a gaban kotun, dan dansa mai gabatar da kara, Insfekta Ibrahim Shuaibu, ya ce an mika mutanen ofishin ’yan sanda na unguwar Tudun Wada ne a ranar 11 ga watan Afrilu, 2022 bayan an kama su.
Ya ce an kama daya daga cikin mutanen ne dumu-dumu yana bayan gida a masallacin, saboda dayan ya yi alkawarin zai ba shi N20,000 idan har ya yi kashi a masallacin.
Wadanda ake zargin dai sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da aikata wa.
Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare su, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu.