An kama shi yana binne layu a fadar Sarkin Kano
Wani mutum mai suna Fatahi Mohammed, mai kimanin shekara 39 da ke Unguwar Sabuwar Gandu a birnin Kano ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta 22 da ke Nomans land a Kano saboda zarginsa da binne layu a Fadar Sarkin Kano.dan sanda mai gabatar da kara Haziel Lidapuwa ya bayyana wa kotun cewa a ranar […]
Wani mutum mai suna Fatahi Mohammed, mai kimanin shekara 39 da ke Unguwar Sabuwar Gandu a birnin Kano ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta 22 da ke Nomans land a Kano saboda zarginsa da binne layu a Fadar Sarkin Kano.
dan sanda mai gabatar da kara Haziel Lidapuwa ya bayyana wa kotun cewa a ranar 17 ga Fabrairun da ya gabata ne wanda ake zargin ya kutsa cikin Fadar Sarki inda ya binne wasu layu da suke kunshe a cikin wata kabewa da ke cike da allurai.
Lokacin da aka karanta masa karar wanda ake zargin ya amsa laifuffukansa, inda dan sanda mai gabatar da kara ya ce laifukan sun saba wa sashi na 342 da na 217 na Final Kod.
Wanda ake zargin ya shaida wa kotun cewa ya binne layun ne don ya yi maganin tsafin da yake zargin abokan kasuwancinsa sun yi masa. Kuma ya ce ya zabi ya binne layun ne a lambun Sarkin kasancewar an umarce shi ya binne layun ne a wurin da ba hayaniya.
Alkalin kotun Mai shari’a Hassan Ahmad ya dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Afrilu mai zuwa kuma ya umarci a tsare wanda ake zargin a kurkuku.