An kama shi yana lalata da gawar buduwarsa da ya kashe zai yi tsafin kudi
Dubun wani matashi ta cika bayan da ya kashe budurwarsa ya yi ta lalata da gawarta na tsawon kwana shida da zummar yin tsafin kudi. ’Yan sanda sun cafke matashin mai shekar 36, wanda ake zargi da kashe budurwar tasa Precious Okeke mai shekara 24, wacce yake zaune tare da ita ne a unguwar Badore […]
’Yan sanda sun cafke matashin mai shekar 36, wanda ake zargi da kashe budurwar tasa Precious Okeke mai shekara 24, wacce yake zaune tare da ita ne a unguwar Badore da ke yankin Ajah Jihar Legas.
- Yadda matar aure ta samu digiri mai daraja ta daya a fannin Lissafi a Jami’ar ABU
- Harin Jirgin Kasa: Mutum 68 na tsare a hannun ’yan bindiga
Matashin ya yi ta yin tsubbace-tsubbacen da bokan ya sa shi tsawon kwanaki shida kafin dubunsa ta cika, bayan kwana shida da ya kashe budurwar tasa.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce wanda ake zargin mai suna Ifeanyi Njoku ya yana hannun hukumar ’yan sandan tare da karin mutum guda da ake zargi da hannu a kisan budurwar mai suna Mbam Atumufor.
Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an tisa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Panti a Yaba.