An kama shugaban karamar hukuma kan yunkurin kashe Shugaban Majalisar Benuwe

Ana zargin shugaban karamar hukumar ya ba wa wasu ’yan bindiga kwangila domin su kashe shugaban majalisar dokokin jihar

An kama shugaban karamar hukuma kan yunkurin kashe Shugaban Majalisar Benuwe

Jami’an ‘Yan sanda

’Yan sanda sun cafke wani shugaban karamar hukuma a Binuwe da ake tuhuma da yunkurin kashe shugaban majalisar dokokin jihar, Aondona Hycenth Dajoh.

Shugaban karamar hukumar yana cikin wasu mutum biyu da ’yan sanda suka cafke kan yunƙurin kashe shugaban majalisar dokokin.

Rundunar ’yan sanda ta ce bincike ya nuna shugaban karamar hukumar ne ya ba wa wasu ’yan bindiga kwangila domin su kashe Honorabul Dajoh.

Kakakin ’yan sanda na kasa, Muyiwa Adejobi, ya sanar ranar Litinin cewa, “Bincike na farko ya nuna cewa shugaban karamar hukumar ya dauki hayar wasu ’yan bindiga domin su hallaka Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Benuwe, Hon. Aondona Hycenth Dajoh.

“Bayan samun sahihan bayanan sirri kan yunkurin kisan, jami’an rundunar leken asiri ta FID-IRT sun yi gaggawar daukar mataki.

“Yanzu dai duk wadanda ake zargin suna hannun ’yan sanda kuma suna bayar da hadin kai ga masu bincike.”

Ya kara da cewa da zarar an kammala bincike, duk wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kuliya.