An kama shugaban ’yan banga da sassan jikin dan Adam
An samu kasusuwa da kokon kai da wasu sassan jikin dan Adam a maboyar ’yan bangan
’Yan sanda sun kama shugaban ’yan banga da kokon kai biyu da wasu sassan jikin dam Adam a Jihar Ribas.
Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa dubun Felix Nwaobakata ta cika ne a yayin aikin samamen da ta kaddamar domin magance wuce gona da iri da ’yan banga ke yi a jihar.
Felix Nwaobakata da aka samu da sassan jikin dan Adam a maboyarsa da ke yankin Omoku da ke a Karamar Hukumar Ogba-Egbema-Ndoni shi ne shugaban kungiyar ’yan banga ta ONELA (OSPAC) a yankin.
Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce an kama wasu mambobin OSPAC bakwai kan zargin aikata kisa da wasu manyan laifuka.
Ya bayyana cewa Nwaobakata shi ne babban wanda ake zargi a kisan wasu mutane biyu ’yan uwan juna a yankin Idu bisa zargin su da laifin garkuwa da mutane a ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
Sanarwar ta ce an dauki matakin taka wa ’yan bangar burki ne sakamakon korafe-korafen jama’a kan yadda suke cin karensu babu babbaka a jihar.
Jami’in ya ce a kwanakin baya ’yan bangar OSPAC sun kai hari Babban Ofishin ’Yan Sanda na yankin Omoku, baya ga fito-na-fito da suke yawan yi da jami’an tsaro a sassan jihar.
“Rana 9 ga watan Mayun 2024 Sarkin Hausawa a yankin ONELGA, Alhaji Usman Seleh, ya kawo kara cewa ’yan OSPAC sun yi garkuwa da wani mutum a cikin al’ummarsa.
“Sakamakon haka ’yan sanda suka gayyaci shugaban ONELGA OSPAC, Felix Nwaobakata, amma ya ki zuwa.
“Maimakon haka, sai kungiyar OSPAC ta kai hari Babban Ofishin ’Yan Sanda na Omoku, amma jami’an da ke ofishin suka fatattake su.
“Bayan nan ne aka kai samame a cibiyar kungiyar da ke Omoku inda muka kama bakwai daga cikin mambobin.
“Daga bisani muka kama shugaban ONELGA OSPAC, Felix Nwaobakata, a ranar 17 ga Yuni, 2023, inda muka same shi da kokon kai guda biyu da kasusuwa da wasu sassan jikin dan Adam.