An kama shugaban ‘Yan fashin da suka shiga banki a Abuja
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kama wani mai suna suna Ernest Ewim, wanda ake tuhumarsa a matsayin shugaban ‘yan fashin da suka shiga banki First Bank a unguwar Mpape da ke Abuja ranar Asabar da ta gabata. Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Anjuguri Manzah, ne ya sanar da hakan, inda ya ce […]
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kama wani mai suna suna Ernest Ewim, wanda ake tuhumarsa a matsayin shugaban ‘yan fashin da suka shiga banki First Bank a unguwar Mpape da ke Abuja ranar Asabar da ta gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Anjuguri Manzah, ne ya sanar da hakan, inda ya ce sun kama saurayin ne mai shekara 29 a maboyarsa da ke Katampe1 a yammacin jiya Laraba.
DSP Anjuguri, ya kara da cewa, a yanzu haka an kama mutum biyar da ke da hannu a aikata yin fashin bankin wadanda suka hada da: ): Ernest Ewim mai shekara 29, Larry Ehizo mai shekara 30, Princewill Obinna mai shekara 24, Timothy Joe mai shekara 21, da kuma Elijah David mai shekara 19.