An kama soja da kwaya a Bauchi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta sanar da kama wani soja mai shekara 34 mai suna Yusuf Gongpolai Adams da tabar wiwi a kan hanyarsa ta kai wa mai saya. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Umar Mamman Sanda ne ya gabatar da wanda ake zargin da sauran wadanda ake zargi a taron manema labarai da aka […]

An kama soja da kwaya a Bauchi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta sanar da kama wani soja mai shekara 34 mai suna Yusuf Gongpolai Adams da tabar wiwi a kan hanyarsa ta kai wa mai saya.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Umar Mamman Sanda ne ya gabatar da wanda ake zargin da sauran wadanda ake zargi a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bauchi.

Rundunar ta ce ta kama wata mota kirar Toyota Highlander ce a wajen Yusuf Gongpolai Adams wanda daga baya ya bayyana cewa shi soja ne da ke aiki a Jihar Abiya.

“Wanda ake zargin yana aiki ne da Rundunar Sojin Najeriya, a Bataliya ta 145, a Jihar Abiya, kuma a yanzu yana wani kwas na ci gaba a Makarantar Kimiyyar Muhalli na Sojojin Najeriya a Jihar Binuwai,” inji shi.

Kwamishinan ya ce za a mika wanda ake zargin ga Hukumar

NDLEA da zarar an kammala bincike.

Sai dai wanda ake zargin ya ce bai san yana dauke da tabar wiwi ne a cikin motarsa ba a lokacin da aka kama shi.

Ya ce, “Ni Mataimakin Kofur ne a soja. Wani abokina ne ya roke ni in taimaka masa in kai wa wani motar, inda ya shaida min cewa ya sayar masa da motar amma bai iya zuwa Benuwai ya dauko ba.”

Ya kara da cewa, “Saboda amincin da ke tsakaninmu ban binciki motar ba.”