An kama soja kan zargin satar makamai a Borno
An kama sojan yana kokarin yin fasakwaurin albarusai 602 daga Jihar Borno
Rundunar Sojojin Najeriya ta kama wani jami’inta mai muƙamin Kofur bisa zargin satar alburusai sama da 600.
Dakarun Rundunar Operation Hadin Kai da ke Maiduguri sun kama Kofur Francis Bako ne a yayin da yake kokarin ficewa daga Jihar Borno da makaman.
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa sojoji masu leken asiri ne suka kama shi ne a tashar motar Kano da ke Maiduguri bayan sun samu rahoto.
Majiyar ta kara bayyana cewa sojan da ya fito daga Malam Fatori yana kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ne a lokacin da aka kama shi da harsashi guda 602 na musamman kirar 7.62mm.
Yanzu haka dai majiyar na cewar sojan yana hannun rundunar domin ci gaba da daukar mataki akan sa musamman dangane da tuhumar da ake masa a kan satar alburusai.