An kama soja kan zargin sayar wa ’yan ta’adda kakin soji
An kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar a Maiduguri, Jihar Borno, yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tserewa zuwa ƙasar Kamaru.
Rundunar Sojin Najeriya ta kama wani jami’inta, Private Mohammed Yusuf, da ake nema ruwa a jallo bisa zargin sayar wa ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka kayan soji.
Rundunar Operation HADIN KAI ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar a Maiduguri, Jihar Borno, yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tserewa zuwa ƙasar Kamaru.
- Akanta Janar zai gurfana gaban Majalisa kan kasafin kuɗin hukumar bogi
- Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai
A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa dakarun 7 Provost ne suka cafke shi a Jidari Bus Stop bayan samun sahihan bayanan sirri.
Tun a ranar 23 ga Yuli ne rundunar ta ayyana Yusuf a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin samar wa ’yan ta’adda kakin soji, tana mai cewa kamen nasa wani gagarumin ci gaba ne a yaƙin da ake yi da ta’addanci.