An kama sojan gona dauke da buhunan wiwi 297

Dubun wani sojan bogi mai suna Akinsola Emmanuel Abiodun ta cika a lokacin da jami’an ’yan sanda suka ci karo da shi a daidai lokacin da yake yi wa wata motar kaya da ke makare da tabar wiwi rakiya a kan hanyar Ibadan zuwa Legas.Sojan gonar dan shekara 29, wanda ya jima yana yin harkar, […]

An kama sojan gona dauke da buhunan wiwi 297
An kama sojan gona dauke da buhunan wiwi 297

Dubun wani sojan bogi mai suna Akinsola Emmanuel Abiodun ta cika a lokacin da jami’an ’yan sanda suka ci karo da shi a daidai lokacin da yake yi wa wata motar kaya da ke makare da tabar wiwi rakiya a kan hanyar Ibadan zuwa Legas.
Sojan gonar dan shekara 29, wanda ya jima yana yin harkar, dubunsa ta cika ne a sa’ilin da yake sanye da kayan soja, dauke da bindigar roba guda biyu, yana ayyana kansa a matsayin soja kamar yadda ya saba.
A lokacin da Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun, Abdulmajid Ali yake gabatar shi a hedikwatar ’yan sandan da ke Eleweron a Abekuta, ya shaida cewa rundunar ’yan sanda ta musanmman mai yaki da ’yan fashi da makami ce ta kame motar kayan, dauke da tabar wiwi, a yayin da direban motar da sauran wadanda ke tare da shi suka tsere, a daidai lokacin da suka ankara da jami’an. A nan suka kame Abiodun bayan da aka duba motar ne sai aka samu buhun tabar wiwi guda 297
Abiodun ya shaida wa Aminiya cewa a garin Aba na Jihar Abiya ya dinka kayan sojin a kan Naira 3,500 kana daya daga cikin bindigogin robar, ya kwace ta ne a hannun wasu ’yan fashi a sa’ ilin da yake taimaka wa ’yan sanda a garin Fatakwal, dayar kuma ya ce ya kwace ta ne daga hannun wata mata mai sayar da kayayyakin wasan yara.
A cewarsa, ya shiga mugunyar sana’ar ne a farkon shekarar 2015, domin ya sami damar tara kudin da zai biya jarabawa, bayan da ya yi karatun difiloma a fannin koyan aikin sojan ruwa.
Ya ce yakan je majami’u a garin Fatakwal a Jihar Kurosriba, inda ake ake ba shi aikin tsaro, inda yakan gayyato wasu jami’an tsaron su yi aikin tare kuma ana biyan su Naira dubu bakwai zuwa goma. Ya bayyana cewa karatun da ya yi ne ya sanya masa sha’awar aikin soja da ma uwa uba son taimaka wa jama’a, domin haka ba ya nadamar danyen aikinsa.