An kama sojoji 3 da kan zargin fashi da garkuwa da mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo ta kama wadansu sojoji 3 da wadansu farar hula bisa zarginsu da sa hannu a cikin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami. Rahotanni sun ce wadanda ake zargin suna cikin jerin wadanda Rundunar ’Yan sanda ta baza koma ta nemansu a yankunan Agenebode da Fugar da kuma wasu […]

An kama sojoji 3 da kan zargin fashi da garkuwa da mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo ta kama wadansu sojoji 3 da wadansu farar hula bisa zarginsu da sa hannu a cikin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Rahotanni sun ce wadanda ake zargin suna cikin jerin wadanda Rundunar ’Yan sanda ta baza koma ta nemansu a yankunan Agenebode da Fugar da kuma wasu sassan jihar, inda aka yi nasarar kama su a ranar Lahadin da ta gabata. Sojojin uku su ne, Kofur Collins Ameh mai lamabr soji 13NA/70/4960 na Runduna ta 3 da ke Jos da Las Kofur Balogun Taiwo, mai lambar soji 13/NA/69/0369 na Bataliya ta 35 da ke Katsina da Kurtu Ebans Isibor, mai lambar 15/NA/73/1529 na Rundunar Sojojin Kasa da ke Owerri, yayin da cikin farar hular da aka kama akwai wani mai suna Goodluck Igbinebor.

Bayanai sun ce Kofur Ameh da Balogun sun taba yin garkuwa da wani mai suna Mista Joseph Otono, a ranar 30 ga Oktoban bana a garin Fugar a Karamar Hukumar Etsako ta Tsakiya, inda daga bisani suka sako shi bayan an biya kudin fansa.

Haka ana zarginsu da yin garkuwa da wata malamar makaranta mai suna Misis Catherine Izuagie, a watan Satumban da ya gabata, inda ita ma suka sako ta bayan da aka biya kudin fansa.

Aminiya ta gano cewa, ’yan sanda sun kama su ne a Jihar Edo, yayin da suke kokarin sayar da wata mota da suka sato daga garin Otono.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar, DSP Chidi Nwabuzo, ya tabbatar da kamun, inda ya ce rundunar tana bincike a kan al’amarin.