An kama sojoji da dan banga sun je karbar kudin fansa
Dubunsu ta cika bayan sun sace wani basarake suna neman miliyoyi a matsayin kudin fansa.
Dubun wasu sojoji su uku da wani dan banga ta cika a lokacin da suka je karbar kudin fansar wani basarake da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna.
An kama su ne bayan sun yi garkuwa da Sarkin kauyen Dorayi, Lawal Ahmed, suka bukaci a ba Naira miliyan uku a matsayin kudin fansa.
Dubun tasu ta cika ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, 2022 bayan ’yan banga sun tsegunta wa sojojin da ke gadi a Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke kan titin Kaduna zuwa Zariya.
Majiyarmu ta ce a lokacin da Sarkin yake hannunsu, sojojin sun nemi ya bayar da kudin fansa Naira miliyan uku, amma daga karshe suka daidaita a kan Naira miliyan daya.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa bayan mutum hudun da aka kama, akwai dan banga daya da ya ranta a na kare.
Mun nemi karin haske daga Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige, wanda ya ce sai ya kammala binciken bayanai game da lamarin.
Sai dai kuma har zuwa lokacin da muke kammala hada rahoton ba mu ji daga gare shi ba.