An kama sojoji na kokarin kai wa ’yan Boko Haram makamai

Wadansu sojoji biyu da suke aiki a karkashin Bataliya ta 143 na sojin Najeriya sun shiga hannu bayan da aka zarge su da taimaka wa mayakan Boko Haram, lokacin da aka kama su dauke da bama-bamai da harsasai za su kai wa ’yan ta’addan.Sojojin biyu an kama su dauke da bama-baman da sauran kayan yaki […]

An kama sojoji na kokarin kai wa ’yan Boko Haram makamai
An kama sojoji na kokarin kai wa ’yan Boko Haram makamai

Wadansu sojoji biyu da suke aiki a karkashin Bataliya ta 143 na sojin Najeriya sun shiga hannu bayan da aka zarge su da taimaka wa mayakan Boko Haram, lokacin da aka kama su dauke da bama-bamai da harsasai za su kai wa ’yan ta’addan.
Sojojin biyu an kama su dauke da bama-baman da sauran kayan yaki ne a a tashar mota ta Yola a lokacin da suke kokarin yin safarar su.
Kakakin Sojin kasa Kanar Sani Usman ya ce abin takaici ne a ce duk da nasarorin da sojojin suke samu, amma a samu kura da fatar akuya a cikin sojojin, wadanda suke tsaye domin ganin su bata suna da martabar sojin Najeriya.
“A ranar Lahadin da ta gabata 7 ga Fabrairu, 2016, wadansu masu kula da bama-bamanmu da suke karkashin Bataliya ta 143, da suka hada da Sapper (Kurtu) Eric Nwokorie mai lamba 13NA/70/10183 da Kurtu Macauley Fortune mai lamba 13NA/70/10263 an kama su a tashar mota ta Yola. An kama su dauke da wadannan kayayyakin soja ba bisa izini ba: Gurneti daya da harsasai masu rai 2,136 samfurin milimita 7.62 (na musamman) da wasu harsasai masu lafiya guda 50 samfurin milimita 7.6 da Makunshin Harsasai guda biyar na bindigar AK47  da kuma harsasan bindiga mai sarrafa kanta,” inji shi.
Kanar Sani Usman, ya kara da cewa: “Sauran kayayyakin da aka kama su da ita sunn hada da gatari daya da adda daya da hula bareti koriya da sutura sanyawa bakwai da bel din soja biyu da rigar shat ta soja guda 12 da rigar ruwa biyu da kwalaben ruwa biyu da takalman ruwa daya da takalmar shiga sahara biyar.”
Ya ce abin takaici shi ne hakan ya faru ne a daidai lokacin da sojoji ke cike da kwarin gwiwa a kokarinsu na mamaye sassa, ta hanyar kai hare-hare da kwanton bauna da sintiri don kawar da birbishin ’yan Boko Haram daga yankin.