An kama sojojin haya daga Najeriya kan yunkurin kashe Shugaban Lesotho
’Yan Sanda a kasar Lesotho sun kaddamar da bincike kan zargin cewa yanzu haka wasu bakin sojojin Najeriya da Ghana su 14 da aka yi hayarsu na yunkurin kashe Firayi Ministan kasar Mista Tom Thabane domin jefa kasar cikin rudanin siyasa. Manyan jami’an ’yan Sandan kasar da jami’an gwamnati sun shaida wa kamfanin Dillancin Labaran […]
’Yan Sanda a kasar Lesotho sun kaddamar da bincike kan zargin cewa yanzu haka wasu bakin sojojin Najeriya da Ghana su 14 da aka yi hayarsu na yunkurin kashe Firayi Ministan kasar Mista Tom Thabane domin jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Manyan jami’an ’yan Sandan kasar da jami’an gwamnati sun shaida wa kamfanin Dillancin Labaran kasar Faransa cewa an kwashe jami’an gwamnati daga ofishinsu yayin da Firayi Minista da Sarki Letsie suka soke aikace-aikacensu.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan kasar Mista Sello Mosili ya ce sun samu labarin cewar an yi hayar sojojin Najeriya da na Ghana 14 domin kashe Firayi Ministan, kuma sojojin hayar sun shiga kasar ce ta yankin Kudu maso Gabas mai kwazazzabai da duwatsu da ke iyaka da kasar Afirka ta Kudu. An ce suna dauke da makamai masu dama.
“Wannan shi ne bayanin da muka samu daga mutanen yankin duwatsun. Kuma har yanzu ana kan bincike,” inji Mosili.
Wani Ministan gwamnatin kasar Thesele Maseribane kuma jagoran jam’iyya ta uku da ke gambizar mulkin kasar ya ce, an janye masu tsaronsa ’yan Afirka ta Kudu daga ofishinsa tun Juma’ar makon jiya kafin isowar sojojin hayar da ke hanyar zuwa kashe shi.
Maseribane ya shaida wa AFP a ranar Litinin cewa, “Ba batu ne na tsarina ko tsaron Firayi Minista, a’a batu ne na tsaron kasa. Shin jama’ata suna da kariya? Amsata ita ce a’a.”
kasar Lesotho tana fama da rikicin iko tsakanin sojoji da ’yan siyasa, inda a ranar 17 ga Oktoba mai shiga tsakani mataimakin Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya shawo kan kwamandan sojan kasar Laftana Janar Tlali Kamoli, ya tafi hutun dole ta barin kasar da zai fara a gobe tare da mika wa mataimakinsa jagorancin sojojin kasar.
Maseribane, ya dora alhakin halin da ake ciki a kasar kan abokan adawa da suke ganin ba za su ci zabe ba don haka suke so rikirkita kasar.