An cafke su suna fim din batsa a wurin ibada
An tsare mazan da matan bayan bullar bidiyon batsar da suka dora a kafar YouTube
Gidajen karuwai
An damke wasu jaruman fim din batsa saboda sun yi fim din jima’i a wani wurin ibada a Jihar Osun.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun ta cafke fitattcen mai fim din batsa, King Tblack, wanda aka fi sani da HOC tare da ’yan wasansa bayan sun yi fim din a wurin ibadar ’yan addinin gargajiya masu bautar Osun, da ke dajin Osun Osogbo na Jihar.
Majiyarmu ta ce Tblack ya yi bidiyon ne tare da jaruman finafinan batsa maza da mata da ya kawo su daga Legas.
Daga bisani HOC ya dora bidiyon a intanet wanda kuma ya karade YouTube.
Bayan bullar bidiyon ne masu bautar Osun suka sanar da limaminsu wanda ya kai kara a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Ataoja.
Sakamakon haka, Babban Baturen ’Yan Sanda Yankin ya tura jami’ansa su nemo Tblack, wanda suka yi nasarar cafko shi tare da jaruman nasa a wani otal a garin Osogbo.
A safiyar Litinin ne Kakakin ’Yan Sanda a Jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da tsare wadanda ake zargin, wadanda ta ce za su fuskanci hukunci.