An kama su da harasan mutane

A ranar Talata jama’a a unguwanni daban-daban na birnin Ibadan suka rika yin binciken kwakwaf ga masu tabin hankali, maza da mata, wadanda ake tababar haukan nasu kuma ake zargin da hannunsu ake gudanar da miyagun ayyuka da suka hada da sace mutanen da ake kashewa ana yin amfani da sassan jikinsu. An yi nasarar […]

An kama su da harasan mutane

A ranar Talata jama’a a unguwanni daban-daban na birnin Ibadan suka rika yin binciken kwakwaf ga masu tabin hankali, maza da mata, wadanda ake tababar haukan nasu kuma ake zargin da hannunsu ake gudanar da miyagun ayyuka da suka hada da sace mutanen da ake kashewa ana yin amfani da sassan jikinsu. An yi nasarar gano wasu sassan jikin mutum har da harasan mutane a cikin tarkacen daya daga cikin mahaukatan. Haka kuma an gano bindiga da adduna da wukake da wayoyin hannu da fiye da Naira dubu 40 a cikin tarkacen mahaukatan.
A dalilin haka ne mutane, a fusace, suka rika yin tururuwa zuwa wuraren da aka kama mahaukatan bogin a inda aka yi musu dukan tsiya da yunkurin cinna musu wuta, amma ’yan sanda suka tserar da su. Duk da haka an kashe daya daga cikinsu, a yayin da jami’an tsaro suka garzaya da masu raunuka zuwa asibitocin gwamnati a Ibadan, kuma akwai daya daga cikin mahaukatan da ke tsare a hannun ’yan sanda.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Oyo, SP Olabisi Okuwobi-Ilobanafor ta tabbatar da aukuwar al’amarin, wanda ta ce an mika duka abubuwan da aka samu a tare da mahaukatan ga sashen bincike (SCID) domin ci gaba da bincike.
Ta ce ’yan sanda ba su iya tabbatar da cewa harasan mutane ne aka samu a cikin kunshin mahaukacin ba, sai idan masu binciken sassan jikin dan Adam sun yi nasu binciken domin gano gaskiyar lamarin.
Kakakin ta yi gargadin mutane su daina yanke wa kansu hukunci, su kyale ’yan sanda su gudanar da aikinsu.