An kama su kan fille kan ɗan acaɓa da sace baburinsa
Kotu ta tsare wasu mutane uku da suka yaudari wani ɗan acaɓa suka fille kansa tare da sace baburinsa
Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Ilọrin, babban birnin jihar Kwara, ta tsare wasu mutane uku da ake zargi da kashe wani ɗan acaɓa tare da sace mashin dinsa.
An gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu ne bisa zargin haɗa baki, sata da kuma cire sassan jikin mutane ba bisa ka’ida ba.
’Yan sanda sun shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a kauyen Asunnara inda aka tsinci gawar wani matashi an guntule kansa a cikin wata mota da misalin karfe 2 na dare.
“’Yan sanda sun gano gawar da kuma wayoyin da ake zargin na wanda aka kashe ne da kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka aikata laifin.
- 6 cikin kowane dalabai mata 10 an ci zarafinsu a jami’o’i 12 —Rahoto
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG
“Ɗaya daga cikinsu ne ya yaudari ɗan acaɓan mai suna Raufu Akanno ya ɗauke shi zuwa unguwar Olooru a kan Naira 10,000 tare da ba shi N5,000.
“A kan hanyarsu, ya bukaci marigayin da ya tsaya, cewa hularsa ta faɗo, dan acaɓan bai sani ba cewa yana shirin yi masa fashi da babur din.
“Daga baya sun buge shi da sanda suka yanke masa kai kafin su sace babur dinsa,” a cewar ɗan sanda mai shigar da kara Nasir Yusuf, wanda ya buƙaci kotun da ta cigaba da tsare waɗanda ake zargin.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Saidu, ya bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Oke Kura, sannan ya ɗage zaman zuwa ranar 23 ga Disamba, 2024.