An kama ta ta hadiye kulli 80 na hodar Iblis za ta kai Saudiyya
Ta shekara tana tara kudin sayen kwayoyin da za ta kai Saudiyya
An kama wata ’yar kasuwa a yayin da take kokarin shiga kasar Saudiyya da kulli 80 na hodar Iblis daga Najeriya.
An kama matar da ke hanyarta ta zuwa Umrah ce a filin jirgi na Abuja, inda aka gano hodar Iblis din a cikin jikinta.
- An rage ranakun aikin gwamnati zuwa kwana 4 a Kaduna
- Najeriya A Yau: Yadda bankuna ke ‘tatsar’ ’yan Najeriya
“Bayan an tsare ta, sai da ta yi bayan gidan kullli 80 da hodar Iblis, tsakanin ranar Laraba zuwa Asabar, 27 ga watan Nuwamba, 2021,” inji mai magana da yawun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) na kasa, Femi Babafemi.
“Matar ta ce ta shekara guda cur tana tara Naira miliyan 2.5 da ta yi amfani da su wajen sayen kwayoyin daga hannun wasu mutum shida daban-daban a Legas.
“A cewar wadda ake zargin, kasuwancin tufafi take yi, kuma sai da ta karbi rancen Naira miliyan daya daga wurare uku ta cika ta sayi kwayoyin, ta kuma kashe kumanin Naira milyan daya wajen sabunta takardar fasfo dinta da samun biza da kudin jirgi,” inji Babafemi.
Jami’an NDLEA sun kama matar mai shekara 46 ne a lokacin da ake cikin tantance fasinjoji kafin su hau wanin jirgin Qatar Airways.
Ta shaida musu a lokacin da suke yi mata tambayoyi cewa wata mata da suka hadu a Umrah a 2019 ce ta ba ta kwarin gwiwar shiga harkar fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasar Saudiyya.
A cewarta, ta shida harkar ce saboda so ta tara Naira miliyan bakwai domin a yi mata aikin dashen maniyyi, kasancewar shekaranta 28 da yin aure amma ba tare da ta samu haihuwa ba, saboda matsalar raunin maniyyi.
Ko a ranar Juma’a 19 ga watan Nuwamba, NDLEA ta kama wani mutum dauke da kulli 101 na hodar heroin a filin jirgin sama da ke Legas, a kan hanyarsa ta zuwa kasar Italiya.
Washegari, 20 ga wata kuma ta kama kwayar khat mai nauyin kilogiram 17.9, da mai shi ya bari a filin jirgin.