An kama ta tana azabtar da ‘yar mijinta
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata matar aure a Unguwar Tarauni a birnin Kano bisa zarginta da cin zarafin ’yar mijinta ta hanyar yayyanka mata jiki saboda tana yawan kashi a kasa. Bayanai sun ce matar mai suna Sakina Muhammad mai kimanin shekara 20 ta dauki tsawon lokaci tana azabtar da ’yar mijin […]
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata matar aure a Unguwar Tarauni a birnin Kano bisa zarginta da cin zarafin ’yar mijinta ta hanyar yayyanka mata jiki saboda tana yawan kashi a kasa.
Bayanai sun ce matar mai suna Sakina Muhammad mai kimanin shekara 20 ta dauki tsawon lokaci tana azabtar da ’yar mijin mai suna Saratu Muhammad a duk lokacin da ta yi mata laifi.
Wata majiya ta ce a wani lokaci Sakina ta kulle yarinyar a daki ta kunna wuta da nufin kone ta, ana cikin haka Allah ya kawo mutanen gidan suka kai wa Saratu dauki.
Matar wacce ’yar asalin Jihar Sakkwaro ce ta bayyana wa Aminiya cewa sharri ake yi mata cewa ta yanka jikin ’yar mijinta, ta ce dukanta kawai ta yi da bulala jikinta ya farfashe.
“Amma ba gaskiya ba ne cewa na yanka mata jiki da reza. Haka kuma kwanaki an ce na kulle ta a daki na kunna wuta don na kone ta, wallahi duk sharri ake yi min,” inji ta.
Sakina wadda take da junan wata hudu, ta dora alhakin faruwar lamarin a kan matar da suke zaman haya a gidanta, mai suna Hajiya Salamatu, “Tunda take yawan yin min kashi matar gidanmu wadda ita ce maigidan take yi min fada wai na kyale yarinya tana yin kashi a ko’ina a gidan ba na dukanta. Idan na gaya mata cewa ai ina yi mata fada ina kuma dan dukanta da hannu sai ta ce ai barkono zan samu na yi mata tsarki da shi ko kuma na samu bulala na rika dukanta da ita. Shi ne wata rana ta samar min bulala ta ba ni ta ce idan ta sake yi min kashi na zane ta da kyau a cewarta ba za ta sake yi ba. Ni kuma ran nan da
Saratun ta yi min kashi sai na bi umarnin Hajiyar inda na dauki bulalar na zane ta da ita. Ni kaina da na ga yadda jini yake fita daga jikin yarinyar sai da tsoro ya kama ni,” inji ta. Ta nuna damuwarta inda ta nemi yarinya Saratu da hukuma su yi mata afuwa.
Mataimakiyar Kwamandar Hisba bangaren mata Malama Zahra’u Muhammad Umar ta ce kasancewar an samu matar da laifin azabtar da ’yar mijinta ta kai ga yayyanka mata jiki za su mika ta hannun Hukumar NAPTIP don yake mata hukuncin da ya dace.
Malama Zahra’u ta yi kira ga mata su ji tsoron Allah su yi hakuri wajen tarbiyyar ’ya’yansu ko na wasu da Allah Ya sallada tarbiyyarsu a hannusu.