An kama ta tana yunkurin yar da jaririyarta
Wata mace mai shekara 21 mai suna A’isha Sani na fuskantar zargin yunkurin yar da jaririryar da ta haifa a bakin hanya a unguwar Pipeline da ke Kubwa, Abuja. Lamarin wanda ya faru a ranar Juma’ar makon jiya, ya jefa mazauna unguwar cikin rudani, sakamakon jini da suka iske a kofar wani shagon aski inda […]

Wata mace mai shekara 21 mai suna A’isha Sani na fuskantar zargin yunkurin yar da jaririryar da ta haifa a bakin hanya a unguwar Pipeline da ke Kubwa, Abuja. Lamarin wanda ya faru a ranar Juma’ar makon jiya, ya jefa mazauna unguwar cikin rudani, sakamakon jini da suka iske a kofar wani shagon aski inda ta haifi jaririn da misalin kafe 3:00 na dare.
Wani mazaunin unguwar mai suna Musa Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewa, wani da ke makobtaka da shagon askin da ta haifi jaririyar ne ya ankarar da jama’a lamarin, a daidai lokacin da ta sanya jaririyar a cikin kwali ta ajiye a kusa da wurin, tana kokarin sulalewa sai mutumin ya rike ta. Musa Ibahim ya ce sun same ta ba karfin jiki, inda ta rika karkawa tare da ci gaba da zubar da jini daga jikinta.
Ya ce mutumin ya garzaya babban ofishin ’yan sanda na Kubwa ya sanar da su al’amarin, ’yan sanda suka zo suka tafi da ita.
Babban jami’in ’yan sandan wanda ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar al’amarin ya ce, sun kai ta babban asibitin Kubwa bayan don kulawa da ita da jaririyar da ta haifa.
Wata jami’ar jinya a sashin mata masu haihuwa a asibitin, ta shaida wa Aminiya cewa, kasancewar jaririyar da ta haifa ’yar bakwanni ce, an sanya ta a kwalba kafin ta yi kwari. Ta ce bayan an kawo matar asibitin ne aka cire mahaifatara da ba ta ida fitowa ba. Ta ce, koda yake ba su ida gano abin da ya yi sanadin haihuwarta kafin lokaci ba, “mu’amala da magungunan zubar da ciki, na iya haddasa haka.”
Ta ce asibitin na kokarin tuntubar sashin walwalar jama’a na Birnin Tarayya don daukan dawainiyar kula da uwar da jaririyarta.
A’isha wadda ta ce ta rabu da mijinta kasa da shekara daya, ta ce ita ’yar asalin garin Gwajo-gwajo ne da ke hanyar Jos daga Keffi. Ta ce tana tare da baffanta a garin Dutsen Alhaji, sai ya bukaci ta bar masa gidansa, bayan ta rabu da mijinta a garin Suleja, suka haifi ’ya’ya uku tare.
Ta ce ba ta yi yunkurin watsi da jaririyarta ba, kuma wanda ya gan ta kukan kaji ya janyo hankalinsa, ba na jaririyarta ba ne.