An kama tela da wasu 30 kan zanga-zanga da tutocin Rasha a Kano

An kama telan ne bayan da aka samu tutocin kasar Rasha guda bakwai a wurinsa.

An kama tela da wasu 30 kan zanga-zanga da tutocin Rasha a Kano

’Yan sanda sun tsare wani tela da wasu muane 30 a Kano kan mallaka da kuma daga tutocin kasar Rasha a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Hedikwatar ’yan sandan Najeriya na zargin telan da dinka dimbin tutocin Rasha da masu zanga-zanga ke amfani da su a Kano da wasu Jihohin Arewa.

Har ila yau, an kama masu zanga-zangar akalla 30 da ke dauke da tutocin, saboda hakan laifin cin amanar kasa ne.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya.

Wasu masu zanga-zangar adawa da mummunan shugabanci a Arewacin Najeriya sun yi ta daga tutar kasar Rasha suna kira gare ta da ta kawo musu dauki.

A karshen makon ne kuma hotunan masu zanga-zangar dauke da tutar Rasha suka yi fara yawo a kafofin sada zumunta.

Hakazalika an ga bidiyon wasu teloli a cikin shago suna dinka tutocin na Rasha, wanda a jikin bidiyon aka rubuta “Gobe babu.”

Washegari, ranar Lahadin Shugaba Tinubu, a jawabinsa ga al’ummar kasar ya gargadi masu zanga-zangar da su guji bari a yi amfani da su wajen cimma wata manufa da ka iya kawo cikas ga cigaban dimokradiyyar Najeriya.