An kama tirela cike da shanun sata
Mutum uku da ke cikin motar shanun satan sun shiga hannu.
’Yan sanda sun kama wata tirela makare da shanun da ake kyautata zaton sato su aka yi a Jihar Kogi.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta cafke tirelar ce a kan titin Lokoja zuwa Kabba bayan da ta ga alamar tambaya a tattare da babbar motar da direbanta.
- Mutum 154 sun bace bayan kifewar jirgin ruwa a Kebbi
- A aikace ya kamata a magance matsalar tsaro —Sarkin Musulmi
- Ta tabbata Zidane zai bar Real Madrid
Kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, DSP Williams Ovye Aya, ya kuma tabbatar da cafke mutum uku a cikin babbar motar mai launin ja.
DSP Aya ya ce a yanzu haka mutanen suna taimakon Rundunar da bayanan da suka dace don kamo ragowar wadanda suke satar shanun mutane tare.
Ya ce da zarar an kammala bincike a kan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a kotu don su girbi abin da suka shuka na laifi.