An kama tsoho kan lalata da ’yar shekara 8

Rundunar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) ta Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani tsoho mai shekara 64 mai suna Idris Auyo bisa zarginsa da yin lalata da ’yar shekara takwas. Kwamandan Rundunar NSCDC na Jihar, Alhaji Muhammed Gidado Fari ne ya bayyana haka a Dutse.Ya ce sun kama tsohon mai suna Idris Auyo ne […]

An kama tsoho kan lalata da ’yar shekara 8
An kama tsoho kan lalata da ’yar shekara 8

Rundunar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) ta Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani tsoho mai shekara 64 mai suna Idris Auyo bisa zarginsa da yin lalata da ’yar shekara takwas.

Kwamandan Rundunar NSCDC na Jihar, Alhaji Muhammed Gidado Fari ne ya bayyana haka a Dutse.
Ya ce sun kama tsohon mai suna Idris Auyo ne da abokin ta’asarsa mai suna Aliyu Mohammed mai shekara 32 a karamar Hukumar Kirikasamma da ke cikin yankin masarautar Hadeja.
Wadanda ake zargin dukansu ’yan asalin karamar Hukumar Auyo ne kuma sun amsa laifinsu ba tare da sun wahalar da rundunar, ba sai dai rundunar ta bukaci a sakaya sunan yarinyar don gudun kada a vata mata rayuwa.
Kwamandan ya ce yarinyar mai shekara takwas likitoci sun tabbatar da an yi lalata da ita, sai dai wadanda ake tuhumar sun nemi a yi musu sassauci. Kwamandan ya ce ana tuhumarsu da laifin aikata lalata da karamar yarinya tare da laifin yin fyade saboda haka za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yi musu hukuncin da ya dace ya kara da cewa daukar matakin abu ne da ya zama dole domin hakan ya zama darasi ga na baya.
Rundunar ta kuma kame almajirai 41 saboda samunsu suna gararamba a kan titi da tsakiyar dare a lokacin da suke aikin sintiri a garin Dutse. Rundunar ta ce sun kame almajiran ne saboda ba su amince da yadda suke yawo da tsakar dare a cikin garin ba.