An kama tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
A watan Afrilun bara aka hambarar da Imran Khan daga mulki.
Rahotanni na cewa an kama tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan a wajen Babbar Kotu da ke birnin Islamabad.
Mista Khan na hanyar halartar zaman kotu, inda ake tuhumarsa da rashawa, wanda ya yi zargin cewa bi-ta-da-kullin siyasa ce kawai.
- Zakarun Turai: Wacce wainar za a toya tsakanin City da Madrid?
- Kotun Koli ta tabbatar da Kawun Davido a kujerar Gwamnan Osun
Hotunan da aka wallafa sun nuna yadda jami’ai sanye da kakin ma’aikatan tsaro, suka kama Mista Khan lokacin da ya shiga harabar kotun, sannan daga bisani suka tafi da shi.
Kamen Khan na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin kasar suka zarge shi da yin wasu zarge-zarge kan wani babban jami’in hukumar leken asiri, Inter-Services Intelligence (ISI).
An gabatar da kararraki goma sha biyu kan dan siyasar mai shekaru 70 tun bayan hambarar da shi daga mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi kokarin tsare shi a lokutan baya amma magoya bayansa suka hana jami’an.
A shekarar da ta gabata, ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai wa ayarin motocinsa a lokacin da yake shugabantar wata zanga-zangar adawa da gwamnati.
Tsohon Firaministan a wani bidiyo da ya fitar ta shafin kamfanin sadarwa na Tehreek-e-Inset (PTI) a manhajar YouTube ya nanata cewa an tsare shi ne bisa zarge-zargen karya da sam bai san da su ba kuma wannan shirin mulkin kama karya ne sabuwar gwamnatin ke shirin yi.
A watan Afrilun bara ne, aka hambarar da shi daga kan mulki, kuma tun daga wannan lokaci yake gangamin ganin an gudanar da zabe a kan lokaci.
A bana, ake sa ran gudanar da babban zabe na kasar.