An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47
Jami’an Rundunar Leƙen Asiri ta musamman a Jihar Kwara sun cafke wani tsohon ɗan gidan yari mai suna Godday Agaadi da bindiga ƙirar AK-47
Jami’an Rundunar Leƙen Asiri ta musamman a Jihar Kwara sun cafke wani tsohon ɗan gidan yari mai suna Godday Agaadi da bindiga ƙirar AK-47.
An kama Emmanuel Okah ne bayan an same shi da bindigar AK-47 da harsashi guda 25 a jikinsa, a lokacin da yake sanye da kayan ’yan sanda.
Dubunsa ta cika ne yana ƙoƙarin satar talotalo a unguwar Omu Aran da ke ƙaramar hukumar Irepodun.
Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya bayyana a taron manema labarai a ƙarshen mako cewa binciken da jami’an suka gudanar ne ya kai ga cafke Agaadi.
- An kama sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulki a Benin
- An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
Ya ƙara da cewa bincike ya ci gaba har ya kai ga kama wasu mutane biyu da ake zargin abokan aikinsa, ciki har da wani boka mai shekaru 41 mai suna Oyeniyi Olabode.
Kwamishinan ya ce babban wanda ake zargi tsohon ɗan gidan yari ne da ke da tarihin aikata laifukan tashin hankali a yankin Omu Aran.
’Ya tabbatar da cewa dukkansu uku suna hannun ’yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran mambobin ƙungiyar.