An kama tsohon shekara 94 kan zargin yi wa yarinya fyade
Tuni ‘yan sandan suka cafke wanda ake zargin yayin da suke ci gaba da bincike a kan lamarin.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta kama wani tsoho mai shekara 94, da ake zargi da yi wa wata karamar yarinya mai shekara 13 fyade.
An kama tsohon ne mazaunin unguwar Tappare da ke Karamar Hukumar Ganye a jihar.
- Muna bukatar allurar rigakafi miliyan 6 don yakar Diphtheria a Kano — Abba
- Kudaden da ministocin Tinubu za su lakume
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Sulaiman Nguroje ya raba wa manema labarai a Yola, babban birnin Jihar, ranar Laraba.
A cewar sanarwar, wanda ake zargin mai sana’ar sayar da maganin gargajiya, ya kasance yana yaudarar yara mata ta hanyar ba su sukari da kayan zaki.
Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Agustan 2023, lokacin da ya kira yarinyar cikin gidansa, inda ake zargin a can ya lalata ta.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu, bincike ya nuna wanda ake zargin a lokacin da yake aikata laifin ya shafa wa wanda abin ya shafa wani turare wanda hakan ya sanya ta fara rashin lafiya bayan faruwar lamarin.
Kakakin ya kuma ce, “Sakamakon rashin lafiya ne lokacin da mahaifiyarta ta tambaye ta, ta bayyana mata abin da ya faru.
“An kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ’yan sanda na Ganye, ta hannun mahaifiyar wanda abun ta shafa.”
Sanarwar ta kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Afolabi Babatola ya nuna takaicinsa kan wannan mumunan lamarin, inda ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da hukunta wanda ya aikata laifin.
“Kwamishinan ’yan sandan ya kuma yi kira ga jama’a musamman iyaye da su kula da unguwanninsu daga masu aikata miyagun laifuka tare da yin taka-tsan-tsan a kokarin rundunar na yaki da kawo karshen duk wani nau’i na cin zarafin mata a jihar.”