An kama tsohuwa kan safarar wiwi da kodin
An kuma kama wasu mutum biyu da kwayoyi sama da kwaya miliyan guda a filin jirgin Legas
An kama wata mata mai shekaru 75 kan safarar miyagun kwayoyi bayan ana kama ta da tabar wiwi da jarkokin kwayar kodin.
Jami’an hukumar NDLEA sun kama ta dauke da jarkoki cike da kodin a unguwar Oshodi a Jihar Legas.
Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya ce ta shaida musu cewa danta da yanzu ake nema ne ya kawo maya kwayoyin ta rika sayarwa.
Hukumar ta kuma kama wasu mutum biyu da kwayoyi sama da kwaya miliyan guda a filin jirgin Legas.
Dayan na dauke da kwayoyi 1,050,000 na tramadol, na biyun kuma rohypnol kwaya 510,000.
- Ghari: An sauya sunan Karamar Hukumar Kunchi
- Kabiru Fagge: Ta’aziyyar tsohon ma’aikacin Muryar Amurka
A Abuja, NDLEA ta kama wani dan shekara 31 da kwalabe 1,496 na kodin a yankin A.Y.A.
A yankin Zuba kuma suka kama wani da kwalabe 400 da ya dauko daga Jihar Ribas.
Wasu matasa biyu kuma tabar wiwi mai nauyin kilo 171 aka kama su da ita a Karamar Hukumar Kaga, Jihar Borno.
A Zamfara kuma an kama wasu uku da kilo 57 a hanyar kauyen Zurmi, matattarar ’yan bindiga.
Jami’an NDLEA sun kuma kama manyan buhuna 35 makare da tabar wiwi a silin din wani dillalinta a unguwar Tudun Kofa, Lafia, Jihar Nasarawa.
A garin Abeokuta na Jihar Ogun an kama kilo 279 na wiwi a cikin buhuna.
Kilo 195 an kama ne a kauyen Karamar Hukumar Orhionmwon, Jihar Edo.
Sai hodar Iblis mai nautin kilo 2.3 da aka kama a hannun wani da Jihar Imo.
Wasu mutun hudu a Jihar Ribas kuma da kwayar Metaphenthamine kilo 127 aka kama su.
NDLEA ce hukumar da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.