An kama uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 5 fyade

Wani magidanci da ya yi wa ’yarsa mai shekara biyar fyade ya shiga hannun ’yan sanda.

An kama uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 5 fyade

Fydae

Wani magidanci da ya yi wa ’yarsa mai shekara biyar a duniya fyade fyade ya shiga hannun ’yan sanda.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta kama magidancin mai shekara 28 ne bayan mahaifiyar yarinyar da aka sakaya sunansu ta kai karar mijin nata zuwa ofishin ’yan sanda

Kakakin rundunar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai kara caji ofis bayan ta lura yarinyar tana jin zafi a matucinta a duk lokacin da take yin fitsari ko ake yi mata wanka idan aka taba gabanta.

Hakan ne ya sa ta tistiye ’yar, wadda ta sanar da ita cewa mahaifinta ne ya kwanta da ita a lokacin da mahaifiyar ta fita unguwa.

Samun wannan korafi ya sa babban jami’in ’yan sanda (DPO) na Ijebu-Mushin ya tura jami’ansa suka kamo mutumi a ranar 22 ga watan nan na Mayu, kuma bai musanta yin lalata da ’yar tasa ba.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Olanrewaju Oladimeji ya bayar da umarnin a tura mutumin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin ci gaba da bincike.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja