An kama uwa da ’ya’yanta masu garkuwa da mutane a Legas
An tona asirin wasu iyali da ake zargi da hada baki wajen yin garkuwa da mutane a lokacin da ’yan sanda a Legas suka yi awon gaba da su. Mutanen wadanda suka hada da Aminay Karimu mai shekara 60 da ’ya’yanta biyu, Akeem Solomon mai shekara 32 da Ojo Solomon mai shekara 26, ana zargin […]
An tona asirin wasu iyali da ake zargi da hada baki wajen yin garkuwa da mutane a lokacin da ’yan sanda a Legas suka yi awon gaba da su.
Mutanen wadanda suka hada da Aminay Karimu mai shekara 60 da ’ya’yanta biyu, Akeem Solomon mai shekara 32 da Ojo Solomon mai shekara 26, ana zargin su ne da laifin yin garkuwa da mutane ta hanyar yaudararsu cewa za su samar masu da aiki mai albashi mai tsoka.
Ana zargin cewa aikin ’ya’yan nata shi ne amfani da kafafen sadarwar zamani na Facebook da Whatsapp, inda ta nan ne suke samun mutanen da suke yaudara. Ita kuma mahaifiyarsu wacce ake zargi gwana ce a fannin bokanci da take da matsayin a sansanin matsafa ta Ifa a Legas, ita ke bai wa ’ya’yanta sa’a, ta hanyar tsafi su samu nasara a kan duk wanda suka hadu da shi a yanar gizo.
An ce sukan gayyaci mutum ne da nufin samar masa aiki kuma da zarar ya je wajensu sai su yi garkuwa da shi, su kira danginsa su nemi a ba su kudin fansa ko su yi barazanar kashe shi.
Asirin matasan da mahaifiyarsu ya to nu ne lokacin da suka yi garkuwa da wani mai suna Osahon Obazee suka nemi danginsa su biya Naira miliyan daya da rabi kafin su sake shi. Kuma suka yi musu kashedi cewa kada su sanar da ’yan sanda; in kuma suka yi haka za su hallaka shi. Duk da wannan kashedin, ’yar uwar wanda aka kame ta sanar da ofishin ’yan sanda da ke Igando a Legas a ranar Juma’ar da ta gabata, kamar yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Edigal Imohimi ya ce.
Ya ce bayan da ’yar uwar ta sanar da ’yan sanda a ranar Juma’a 7 ga Satumba da misalin karfe 4 na yamma, “Nan take na bai wa jami’an shiyyar Igando umarnin bibiyar lamarin tare da gudanar da bincike, inda aka gano wadanda ake zargin aka kama su tare da kubutar da karin wadansu mutum biyu masu suna Fadugbagbe Akindele da Ekwegbalu Augustine, wadanda suka yaudara ya zo tun daga Jihar Anambra, bayan sun yi masa alkawarin samar masa aiki mai albashi mai tsoka a kamfanin man fetur,” inji Kwamishinan.
Ya ce tuni hukumarsu ta hada wadanda aka kubutar da ’yan uwansu, kuma za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
daya daga cikin ’ya’yan nata ya shaida wa ’yan jarida cewa mahaifiyarsu ce take taimaka musu wajen tsafe wadanda suke hulda da su a kafafen sada zumunta na yanar gizo, kuma tana amfani da tsafin nata wajen tsorata duk wanda suka yi garkuwar da shi.