An kama uwa tana lalata da dan cikinta a gona
Danta na fari ya shafe shekara bakwai yana lalata da ita.
Dubun wata mata da ke lalata da ’ya’yan cikinta bayan rasuwar mahaifinsu ta cika bayan fada ya kaure tsakanin ’ya’yan nata a kanta a Jihar Kwara.
Binciken Aminiya ya gano cewa matar ta haifa wa danta na fari ’ya’ya uku, kafin daga bisani ya kama ta da kaninsa suna tsaka da lalata a cikin gona.
- Kisan direban tashi: Kotu ce za ta raba mu da sojoji —Iyalai
- Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 54 —MDD
A ranar Lahadi da ta gabata ne hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta tabbatar da cafke matar da babban danta nata, a yayin da ake ci gaba da neman daya dan nata, wanda ya cika bujensa da iska.
A binciken da Aminiya ta gudanar, ta gano cewa mahaifiyar tasu ta haifi ’ya’ya 11 da mijinta kafin rasuwarsa, daga baya kuma ta haifi ’ya’ya uku da danta na fari.
Wata majiya ta bayyana cewa, ’ya’yan nata biyu sun fara samun matsala, har da ba wa hamata iska ne bayan babban dan ya kama uwar da kaninsa suna tsaka da lalata, turmi da tabarya, a cikin gona.
Majiyar ta kara da cewa, “Babban dan ya gano yadda mahaifiyarsu take kebewa da kaninsa suna lalata, wanda hakan ya haifar da mummuna sabani a tsakaninsu, har ta kai ga sun fara fada, lamarin da ya jawo hankalin masu gonakin da ke kusa.
“NSCDC ta kama babban dan da mahaifiyar tasu a farfajiyar Moshe Gada a Karamar Hukumar Kaiama. Daya dan kuma ya tsere”.
Da yake magana kan lamarin a ranar Litinin, kakakin NSCDC, Babawale Zaid Afolabi, ya ce, “Bayan gudanar da bincike an mika matar da dan nata na fari ga jami’an kasar Jamhuriyar Benin da ke kan iyaka, saboda mutanen ba ’yan asalin Najeriya ba ne.
“A yayin da ake gudanar da bincike, dan na fari, ya bayyana cewa ya yi kimanin shekara bakwai yana saduwa mahaifiyar tasa.”