An kama wadanda ake zarginsu da kisan dan sanda a Bayelsa

Hukumar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tsare mutum 4 da ake zarginsu da kashe jami’in dan sanda wanda ke aiki da sashin dakile ta’addanci a Unguwar Tombia da ke karamar Hukumar Yeneguwa babban birnin jihar. Kwamishinan ‘yan sanda Mista Joseph Mukan, ne ya sanar da hakan a Hedkwatar ‘yan sandan jihar. Inda ya ce, a […]

An kama wadanda ake zarginsu da kisan dan sanda a Bayelsa

Hukumar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tsare mutum 4 da ake zarginsu da kashe jami’in dan sanda wanda ke aiki da sashin dakile ta’addanci a Unguwar Tombia da ke karamar Hukumar Yeneguwa babban birnin jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda Mista Joseph Mukan, ne ya sanar da hakan a Hedkwatar ‘yan sandan jihar. Inda ya ce, a ranar 21 ga watan Oktoba 2018 hukumar ta tsare daya daga cikin wanda ake zargi mai suna Funkeye John Timbofa wanda ya yi sanadiyyar hanyar kama mutum 4 da ake zarginsu da aikata kisan.