An kama wadanda suka kai harin ranar Ashura a Saudiyya
Mutum 11suka rasu a harin da aka kai a gundumar Al-Ahsa da ke gabashin Al-Shakra a kassim da ke kasar Saudiyya. Maharan dai sun kai wannan harin ne ga masu bikin ranar Ashura. Tuni dai wadanda ake zargi da kai harin suka shiga hannu. “Mutum bakwai aka kashe, kuma aka jikkata wasu mutum bakwai din, […]
Mutum 11suka rasu a harin da aka kai a gundumar Al-Ahsa da ke gabashin Al-Shakra a kassim da ke kasar Saudiyya. Maharan dai sun kai wannan harin ne ga masu bikin ranar Ashura. Tuni dai wadanda ake zargi da kai harin suka shiga hannu.
“Mutum bakwai aka kashe, kuma aka jikkata wasu mutum bakwai din, alokacin da mahara masu dodon fuska suka bude wagungun mazaunan garin Dalwah wuta a yahnkin Al-ahsa,” a cewar Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya, Manjo Janar Mansour Al-Turki.
“Mutum 15 da ke da hannu a kai harin sun shiga hannun ‘yan sanda, a daidai lokacin da suka kai irin wadannan hare-haren a birane shida, wadanda suka hada da Shakra da ke gundumar kassim da Al-Ahsa da Alkhobar a gabashin kasar,” inji Al-Turki.
Ya ce a wannan harin da suka kai Shakra sun halaka jami’an tsaro biyu,inda biyu daga cikin maharani su ma suka kwanta dama. Jami’an tsaron da aka kashe sun hada da Kyaftin Mohammad Al-Enezi da Kofural Turki Al-Rasheed.
Wani da al’amarin ya auku a gabansa, yabayyana wa ’yan sanda cewa ’yan sanda sun farmaki maharani a kauyukan da suka hada da Al-Jeffer da Taraf da Jesha.