An kama wadanda suka kashe Janar din Soja a Abuja
Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, ne ya gabatar da wadanda aka zargin da kashe Birgediya-Janar Uwem Udukwere a gidansa da ke Sunshine Estate
’Yan sanda sun kama ’yan fashin da ake zargi da kashe wani tsohon soja mai mukamin Birgediya-Janar a Abuja.
Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ne ya gabatar da wadanada aka zargin da kashe Birgediya-Janar Uwem Udukwere a gidansa da ke Abuja.
A ranar Asabar ne ’yan fashi suka kutsa gidan Birgediya-Janar Uwem Udukwere da ke rukunin gidajen Sunshine Estate, da misalin karfe 3 na dare suka hallaka shi.
Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa bindigar janar din sojan da aka kashe na hannun ’yan fashin biyu da su tsere, wadanda yanzu ake nema ruwa a jallo.