An kama wadanda suka kware wajen kisan kai a Gombe
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta gabatar da wasu mutum shida ga manema labarai da take zargin sun yi kaurin suna wajen aikata kisan kai da yi wa mata fyade tare da kwace musu gwala-gwalai da wayoyin hannu. Da yake yi wa manema labarai karin haske kan matasan a Gombe, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Abdullahi […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta gabatar da wasu mutum shida ga manema labarai da take zargin sun yi kaurin suna wajen aikata kisan kai da yi wa mata fyade tare da kwace musu gwala-gwalai da wayoyin hannu.
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan matasan a Gombe, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Abdullahi Kudu Nma, ya ce sun jima suna farautar matasan ba su kama su ba sai yanzu.
“Dama masu laifi ne da muka dade muna son mu kama su domin sun aikata laifuffuka daban-daban sun gudu amma yanzu Allah Ya ba mu sa’a mun kama su bayan sun dawo gari,” inji Kwamishinan.
Kwamishina Kudu Nma, ya ci gaba da shaida wa ’yan jarida cewa “Ku bar ganinsu kanana, manyan miyagu ne domin da kansu ba mu matsa su ba, suka gaya mana irin laifuffukan da suka aikata kuma za ku iya tambayarsu don ku tabbatar.”
Ya ce daya daga cikinsu mai suna Abdulraham Abubakar da ake yi wa lakabi da Loos Time ba karamin hadari ba ne a jihar domin yana cikin wadanda suka addabi mutanen yankin Unguwar Pantami, kuma ya ce yana tawaga har guda biyar wadanda shi ne shugabansu, kuma ba su da aikin yi sai kisa da yi wa mata fyade su kwace jakankuna da wayoyinsu idan suka ki su soke su da wuka.
Kwamishinan ya ce Abdulkadir Musa mai lakabin Kani Awu tun bara ya yi kisan kai ya gudu sai yanzu ya shiga hannu.
Sai ya yi kira ga iyaye cewa su rika bai wa ’yan sanda hadin kai da cikakken goyon baya musamman mazauna Unguwar Pantami da suke bai wa ’yan sanda ciwon kai idan
’ya’yansu sun aikata laifi suka shiga gida sai su boyesu su hana ’yan sanda shiga gidan su kama su.
Da wakilinmu ya tambayi Abdulraham, Loos Time ya tabbatar da cewa ’yan sanda sun kama su ne kan laifin kisan wani mai suna Alhaji Kwalke da suka kashe a Unguwar Idi suka gudu inda shi ya tsere zuwa Katsina wajen yayansa.
Ya ce fada ne na unguwa da unguwa ya hada su, shi ne suka taru suka kashe Alhaji Kwalke ta hanyar daba masa wuka a ciki.
Matasan da aka kama su ne Abdulkadir Musa da Abdulraham Abubakar da Ishiyaku Ali mai lakabin Safina, sai Nasiru Ahmed da ake kira Nani da Ayuba Ibrahim da ake kira Obolo da kuma Okasha Abubakar da ake kira Wurle.