An kama wadanda suka lakada wa dan Najeriya duka a Indiya
’Yan sanda a Delhi babban birnin Indiya sun ce sun kama mutum biyar wadanda ake zargi da yi wa wani dan Najeriya dukan kawo wuka. A ranar Talata ne kafofin watsa labarai a Indiya suka nuna bidiyon da ke nuna yadda wasu gungun Indiyawa suka lakadawa wani dan Najeriya duka a birnin Delhi. BBC ta […]

’Yan sanda a Delhi babban birnin Indiya sun ce sun kama mutum biyar wadanda ake zargi da yi wa wani dan Najeriya dukan kawo wuka.
A ranar Talata ne kafofin watsa labarai a Indiya suka nuna bidiyon da ke nuna yadda wasu gungun Indiyawa suka lakadawa wani dan Najeriya duka a birnin Delhi.
BBC ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun tsare mutumin Najeriyar wanda ayarin wasu magidanta a Delhi suka zarga da sata.
A cikin bidiyon, an ga mutane guda hudu ko biyar na amfani da sanduna suna rafka wa mutumin, bayan an daure shi a jikin wani turke.
Ko lokacin da yake roko Allah-Annabi a yi masa afuwa wani mutum ya kama kafafuwansa, inda wani ya rika zane shi a tafukansa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun afkuwar irin wannan lamari ba a Indiya, ko a watan Afrailun da ya gabata ma an kai wa wasu dalibai ’yan Najeriya hari a Delhi, inda aka musu duka.
A wancan lokacin har sai da jakadun kasashen Afirka a Delhi suka yi Allah wadai da hare-haren da aka kai din.
Kazalika an sha kai wa ’yan wasu kasashen Afirka da dama hari a sassa daban-daban na Indiya.
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne aka nuna bidiyon Indiyawan suna lakadawa dan Najeriyan. Tashar talabijin ta NDTb da ke Indiya ta bada rahoton cewa mazauna unguwar ne suka tuhumi mutumin da yin sata a cikin wani gida.
Daga baya sun mika dan Najeriyan ga jami’an ’yan sanda bayan wannan harin, kuma an ga rauni a kansa da fuskarsa da kafafunsa har ma da bayansa, inji rahotan.
’Yan sanda sun sanar da tashar NDTb cewa sun gurfanar da dan Najeriyan a gaban wani alkali bayan da aka duba lafiyarsa a asibiti, kuma alkalin ya bada umarnin a tsare shi a kurkuku.