An kama wadanda suka yi garkuwa da mai gidansu suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa
Yan Sanda a Jihar Oyo sun kama mutum 5 da suka yi garkuwa da mai gidansu Sunday Aladeniyi suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa Naira dubu 700 daga iyalinsa. Hudu daga cikin mutanen da aka kama Fulani ne masu suna Abdullahi Musa da Yuguda Yusuf da Isah Tambaya da Aminu Ahmadu da jagoransu […]
Yan Sanda a Jihar Oyo sun kama mutum 5 da suka yi garkuwa da mai gidansu Sunday Aladeniyi suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa Naira dubu 700 daga iyalinsa.
Hudu daga cikin mutanen da aka kama Fulani ne masu suna Abdullahi Musa da Yuguda Yusuf da Isah Tambaya da Aminu Ahmadu da jagoransu John Ojo. Dukansu suna aiki ne a gonar kiwon kaji mallakar ubangidan nasu.
Da yake nuna mutanen ga ’yan jarida a ofishinsa a Ibadan, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude ya ce wadanda ake zargin sun sace Sunday Aladeniyi ne daga gonar kiwon kajinsa da ke kauyen Onigambari a hanyar Ijebu-Ode. Bayan sun karbi kudin fansa Naira dubu 700 sai suka bindige shi, suka binne gawar a dajin Gwamna da ke hanyar Ibadan zuwa Ijebu-Ode. Binciken ’yan sanda ya tabbatar da cewa mutanen sun bindige mai gidan nasu ne bayan sun fahimci ya gane daya daga cikinsu.
Ya ce iyalan marigayin ne suka kai rahoton bacewar Mista Sunday Aladeniyi zuwa ofishin ’yan sanda na Idi Ayunre inda nan take sashen yaki da masu garkuwa da mutane (AKS) ya fara aikin bincike ya yi nasarar kama su tare da gano gawar mutumin.
Kuma ya nuna wani mutum, mai suna Adebisi Kayode da ke sojan gona a matsayin sufeton ’yan sanda, inda ya karbi fiye da Naira miliyan 2 daga hannun mutane daban-daban da sunan zai taimaka musu wajen samun gwanjon motoci da wasu kaya da ’yan sanda suke yi. An samu ankwa guda daya da katunan wayar salula da tsabar kudi tare da dan sandan bogi da ake zargin yana amfani da su wajen damfarar mutane.
Mutum 19 aka nuna wa ’yan jarida da aka kama su kan zargin aikata laifuffukan fashi da makami da sata da tsafe-tsafe da yaudara da makamantansu. Kwamishinan ya nuna bindigogi 2 da albarusai 4 da kananan motoci 3 da wayoyin salula 9 da wukake 2 da adda 1 da kwarya mai dauke da kayan tsafi da aka samu a hannun mutanen da aka kama.
Dukan wadanda ake zargi da aikata miyagun ayyukan sun amince da aikata laifin da ake zargin sun yi. Kwamishinan ya ce za a gurfanar da su gaban shari’a da zarar an kammala bincike.