An kama wadanda suka yi garkuwa da ‘yan yi wa kasa hidima

Sashin dakile masu garkuwa da mutane na hukumar ‘yan sandan jihar Imo sun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da masu yi wa kasa hidima NYSC biyar. An yi garkuwa da ‘yan yi wa kasa hidima biyar ne a yankin Umuapu da ke hanyar Owerri zuwa Fatakwal a ranar 23 ga Oktoba 2018 a […]

An kama wadanda suka yi garkuwa da ‘yan yi wa kasa hidima

Sashin dakile masu garkuwa da mutane na hukumar ‘yan sandan jihar Imo sun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da masu yi wa kasa hidima NYSC biyar.

An yi garkuwa da ‘yan yi wa kasa hidima biyar ne a yankin Umuapu da ke hanyar Owerri zuwa Fatakwal a ranar 23 ga Oktoba 2018 a hanyar su ta zuwa sansanin horar da masu yi wa kasa hidima NYSC na jihar Ribas da jihar Akwa Ibom.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo Dasuki Galadanchi, ya bayyana wa majiyar mu cewa, a yau Laraba ne ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da ‘yan yi wa kasar hidima bayan wani bincike na musamman da suka qaddamar.