An kama wadanda suka yi wa Shugaban Kwamitin Binciken Rikicin Ombatse fashi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta sake samun nasarar cafke ’yan fashi da makami 22 ciki har da wadanda suka kwace motar Shugaban Kwamitin Bincike a kan kisan gilla ga jami’an tsaro da ’ya’yan kungiyar matsafa ’yan kabilar Eggon da aka fi sani da Ombatse suka yi a kauyen Alakyo da ke jihar.Kwamishinan ’Yan sandan […]

An kama wadanda suka yi wa Shugaban Kwamitin Binciken Rikicin Ombatse fashi
An kama wadanda suka yi wa Shugaban Kwamitin Binciken Rikicin Ombatse fashi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta sake samun nasarar cafke ’yan fashi da makami 22 ciki har da wadanda suka kwace motar Shugaban Kwamitin Bincike a kan kisan gilla ga jami’an tsaro da ’ya’yan kungiyar matsafa ’yan kabilar Eggon da aka fi sani da Ombatse suka yi a kauyen Alakyo da ke jihar.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Umar Shehu ne ya sanar da haka a hedikwatar rundunar a Lafiya a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai.
A cewarsa an gano motar shugaban kwamitin ce a garin Oturkpo a Jihar Benuwai da ke makwabaka da jihar, kuma an gano bindigogi kirar harba-ka-ruga guda hudu da wasu makamai da adduna da bindigogin roba daga wadanda ake zargin.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce an yi nasarar kama ’yan fashi ne sakamakon himmar rundunar na kawo karshen aikata miyagun ayyuka a jihar. Umar Shehu ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a wurare daban-daban a sassan jihar. Ya ce “Mun samu nasarar cafke wadanda suka saci motoci bakwai a Lafiya. Sauran kuma a garin Keffi da Mararraba da Akwanga, kuma an kama su ne da bindigogi da alburusai.”
Sai ya ba da tabbacin cewa rundunar ta dauki kwararran matakan don ci gaba da kama batagari a jihar da kuma hukunta su, kuma ya nemi hadin kan al’ummar jihar don kawo karshen aikata miyagun ayyuka a jihar.
Kimanin mako uku da suka gabata ne ’yan fashi suka kwace motar aiki da gwamnatin Jihar Nasarawa ta ba Shugaban Kwamitin Binciken Kisan Jami’an Tsaro da ’Yan kungiyar Ombatse suka yi Mai shari’a Joseph Bola Gbadeyon a kan hanyarsa ta zuwa inda ake zaman sauraren bahasin wannan kisa suka gudu.  ’Yan sandan sun ki amince cewa ’yan fashi da makami sun kwace motar shugaban a lokacin da lamarin ya auku, amma bayan ta kama wadanda ake zargin sai ta gabatar da su ga manema labarai a matsayin ’yan fashi.