An kama wanda ake zargi da kashe makwabcinsa kan akuya

Allah Ya tona asirin wani mutum da ke kauyen Fanisau a karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa da ’yan sanda suka jima suna nema bisa zarginsa da kashe makwabcinsa saboda a cewarsa, mamacin ya zarge shi da sace masa akuya. Kakakin ’Yan sandan  Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce […]

An kama wanda ake zargi da kashe makwabcinsa kan akuya
An kama wanda ake zargi da kashe makwabcinsa kan akuya

Allah Ya tona asirin wani mutum da ke kauyen Fanisau a karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa da ’yan sanda suka jima suna nema bisa zarginsa da kashe makwabcinsa saboda a cewarsa, mamacin ya zarge shi da sace masa akuya.

Kakakin ’Yan sandan  Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin mai suna Iliyasu Saleh ya hallaka Muhamed Ubale ne da duka da sanda, shi da wani dansa mai suna Datti Saleh lokacin da ya je gidansa neman awakinsa da suka bata. Kuma bayan sun hallaka shi, sai suka jefa gawarsa a cikin rijiya gudun kada asirinsu ya tonu.

A yayin da ’yan sanda suka je gidan Iliyasu bincike, sun samu wasu bindigogi kirar harbi-ruga masu tashi sau biyu, lamarin da ya sa suka shiga tuhumarsa, cewa yana daya daga cikin mutane masu aikata miyagun ayyuka da suka addabi jama’a a karamar Hukumar Dutse. Jinjiri ya kara da cewa asirin Iliyasu da dansa Datti ya tonu ne sakamakon ihu da shi Ubale Muhammed ya yi kuma ba a gan shi ba, sakamakon haka matarsa ta sanar da ’yan sanda halin da ake ciki; daga baya ne aka gano gawarsa a cikin wata rijiya.

Sakamakon haka ne wadanda ake zargin suka gudu zuwa Jihar Benuwai, har sai da aka dauki lokaci sai Iliyasu ya kawo ziyara gida, inda aka tsegunta wa ’yan sanda inda suka kama shi.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan da aka gabatar da shi a gaban ’yan jarida, Iliyasu ya amsa laifinsa cewa shi ne da dansa suka hallaka Ubale. Sai dai ya ce marigayin ne ya zo rugarsa ya kama shi da duka haka kawai, inda sakamakon haka ne shi da dansa suka yi masa duka har ya mutu, lamarin da ya sa suka jefa gawar a rijiya.

Ya kara da cewa maganar bindigogi kuma da aka samu a wurinsa, yana amfani da su ne domin kare dabobinsu daga barazanar barayi ko wadansu miyagun namun daji a lokacin kiwo.