An kama wanda ake zargi da kisan mawaki Tupac shekaru 27 da suka wuce

Tun a 1996 aka kashe shi, amma ba a gano wanda ya kashe shi ba

An kama wanda ake zargi da kisan mawaki Tupac shekaru 27 da suka wuce

An kama wani mutum da sanyin safiyar Juma’a a Amurka bisa zarginsa da kisan mawakin nan da ya shahara a kidan gambarar zamani (Hip-hop), Tupac Shakur, tun a shekarar 1996.

Wani mutum da ke kan mota ne dai ya harbe Tupac a birnin Las Vegas na Amurka, bayan ya kammala wani wasa.

Kafar yada labarai ta ABC News da ke Amurka ta rawaito cewa wanda ake zargin yanzu haka yana can yana amsa tambayoyi a hannun jami’an tsaro.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba za a bayyana tuhume-tuhumen da ake wa mutumin a ranar dai ta Juma’a.

Tupac, wanda ya yi tashe a lokacin da yake raye, an harbe shi ne a ranar bakwai ga watan Satumbar 1996 a Las Vegas, bayan kwana shida da faruwar lamarin kuma ya mutu a asibiti yana da shekara 25 a duniya.

Tun lokacin ne dai ake ta kokarin bincike domin gano wanda ya kashe shi, amma abin ya ci tura.

Ko a watan Yulin da ya gabata sai da ’yan sanda suka kai samame a wasu gidaje da ke birnin na Las Vegas domin binciken.

Yanzu haka dai mutumin na can a hannun jami’an tsaro ana tsare da shi, bayan da suka kama shi lokacin da yake tafiya kafa.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano