An kama wanda ake zargi da yi wa jaririya ‘yar wata uku fyade

Rundunar Samar da Kariya Ga Fararen Hula (NSCDC) ta kama wani mutun bisa zargin yin fyade ga wata yarinya ‘yar shekaru uku a jihar Nasarawa. Da yake gabatar da wanda ake zargin ga ‘yan jarida a lafiya, Mataimakin Kwamandan Rundunar a jihar Nasarawa Bisi Olugboyega, ya ce an kama mutumin ne a gidansa da ke […]

An kama wanda ake zargi da yi wa jaririya ‘yar wata uku fyade

Wanda ake zargin bayan an kama shi

Rundunar Samar da Kariya Ga Fararen Hula (NSCDC) ta kama wani mutun bisa zargin yin fyade ga wata yarinya ‘yar shekaru uku a jihar Nasarawa.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga ‘yan jarida a lafiya, Mataimakin Kwamandan Rundunar a jihar Nasarawa Bisi Olugboyega, ya ce an kama mutumin ne a gidansa da ke kauyen Adogi a Karamar Hukumar Lafiya inda a nan ne ya aikata wannan badalar.

Ya ce an aikata irin wannan fyade a yankin to amma ba a taba yin nasarar kama masu aikatawa ba sai a wannan karon.

Mataikin Kwamandan ya ce rundunar za ta gurfanar da wanda take zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa sai dai ya ce ba shi kadai ke yi wa kananan yara fyade ba.

A kwanankin baya ba, Aminiya ta kawo muku labarin yadda a jihar Nasarawa wani wanda ba a san ko wane ne ba ya bi cikin dare ya dauke jaririya a hannun uwarta tana barci, inda daga baya aka tsinci yarinyar ya lalata ta.

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, mahaifiyar jaririyar ‘yar wata uku da aka yi wa fyaden ta ce ranar 27 ga watan Mayu ce suna barci a tsakar gida saboda zafi daga bisani suka shiga daki da ‘yar tata, amma saboda tsannanin zafi ba ta rufe kofar dakinta ba. Bayan ta farka da misalin karfe uku na dare sai ta ga babu diyarta a wurin da suke kwance tare.

Hakan ya birkita ta sai ta tafi wurin mahaifin mijinta ta fada masa cewa ita fa bata ga jaririyarta ba, ya tambaye ta yaya hakan ya faru, ta fada masa.

An yi wa jaririyar jinajina, an jefar da ita kango

Daga nan da ita da surukin nata da dangi da sauran mutanen kauyen na Adogi suka bazama neman yarinyar inda aka gano ta a kangon wata makarantar sakandaren kauyen dauke da raunuka da jini ko ina a jikinta.

Mahaifiyar yarinyar ta ce bayan samun ‘yar tata sai suka garzaya da ita zuwa karamin asibitin yankin amma jami’an asibitin suka ce yanayin da yarinyar ke ciki ba za su iya duba ta ba sai dai a wuce da ita zuwa asibitin kwarrarru na Dalhatu Araf da ke Lafiya Babban Birnin jihar.

Ta ci gaba da cewa bayan sun kai ta asibitin kwarrarrun ne likitocin suka duba ta suka ce za su iya yi mata aiki to amma daga bisani bayan sun kammala sayen magunguna kuma ana dab da shigar da ita dakin tiyata domin yi mata aiki sai likitocin suka ce ba za su iya ba saboda raunuka da aka yi mata sun shafi farji da hanjinta baya ga sauran sassan jikinta.

‘Sai da na sayar da katifata na biya kudin magani’

Mahaifiyar yariyar ta cigaba da cewa, “Daga asibitin kwarrarru na Lafiya an tura mu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos kuma bayan mun tafi Jos likitocin asibitin sun duba sun ce za a iya yi mata aiki.
“Sai dai mun kasance ba mu da kudin zuwa asibitin Jos saboda mun riga mun kashe kudadenmu a asibitin Lafiya duk da haka dai mun yi kokari mun samu naira dubu ashirin to amma an ce mana ba zai isa ba sai da na sayar da katifar kwanciyarmu na kara kudin a kai kafin muka je asibitin.

“Zuwanmu Jos likitoci sun yi mata aiki a sassa biyu na jikinta wato hanji da farjinta kuma asibitin sun ba mu mako biyu mu dawo don su yi mata aiki na uku”

Allah ne zai saka mana

Mahaifiyar jaririyar ta ce mijinta baya nan a lokacinda lamarin ya faru, “yana can garin Sapele na jihar Delta ya bayyana damuwarsa matuka to amma ya ce babu wani abin da zai iya yi a kai sai dai ya bar wa Allah”, inji ta.

A wannan lokacin al’amuran yi wa kananan yara da mata fyade na kara daukar hankulan jama’a a Najeriya.