An kama wanda ake zargi da yi wa yarinya goyo da bam a Funtuwa

A ranar Talata da dare ne wasu jama a Unguwar Tudun Wada Funtuwa suka samu nasarar kama wani da ya je unguwar da wata mota kirar Jeep Honda CRb mai lambar Adamawa, Michika (MCH 793) dauke da wata yarinya ’yar shekara 10 kuma ake zargin ya yi kokarin goya mata bam domin tayar da shi. Jama’ar […]

An kama wanda ake zargi da yi wa yarinya goyo da bam a Funtuwa
An kama wanda ake zargi da yi wa yarinya goyo da bam a Funtuwa

A ranar Talata da dare ne wasu jama a Unguwar Tudun Wada Funtuwa suka samu nasarar kama wani da ya je unguwar da wata mota kirar Jeep Honda CRb mai lambar Adamawa, Michika (MCH 793) dauke da wata yarinya ’yar shekara 10 kuma ake zargin ya yi kokarin goya mata bam domin tayar da shi.
 Jama’ar sun baka wa motar wuta inda ta yi kara mai tsanani da ake zaton fashewar wasu bama-bamai ne da ke cikinta.
Aminiya ta jiyo daga mutanen da suka gane wa idonsu lamarin cewa da misalin karfe 10:00 na dare wasu jama’ar suka ga motar a wajen wani masallaci, kuma sun fara zargi a kanta ne, bayan da suka ga an fito da wata yarinya kuma mutumin na daura mata wani abu da ba su fahimta ba.
Majiyarmu ta ce jama’a sun tunkari wurin mota kuma ganin haka mutumin ya gudu suka bi shi, wasu suka nufi yarinyar wadda ganin abin da ke tare da ita ya firgita su, nan take suka kwance abin da ake zaton bam ne.
Majiyar ta ce, yarinyar wadda alamu suka nuna ba ta cikin hayyacinta, ta ce daga Kano aka sato ta, amma ta kasa yin karin bayani.
Shi kuma mutumin da ya yi kokarin tserewa an kamo shi kuma jama’a suka rika bugunsa kafin isowar jami’an tsaro.
Wata majiya ta ce, yadda aka rika gudu da motar a cikin gari ne ya janyo hankalin jama’a suka yi yunkurin tsayar da direban motar a daidai masallacin shi kuma ganin haka ya fito ya tsere.
Ita kuma yarinyar ta nemi taimakon jama’a inda a nan ne aka gan ta dauke da abin da ake zaton bam ne aka yi hanzarin kwance mata aka jefar a cikin wani rami da ke gefen hanya.
Aminiya ta jiyo cewa mutane da dama sun kaurace wa gidajensu a daren don rashin sanin abin da ka iya faruwa musamman jin cewa an jefar da abin da aka kwance daga jikin yarinyar da aka kiyasta shekarunta daga 10 zuwa 12 a cikin wani rami.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin ’yan Kakakin ’Yan Sandan Jihar Katsina inda ya ce, suna wani taro, kuma daga baya ya sake kiransa bai dauki waya ba.