An kama wanda ke sayar da ’ya’yansa a Nasarawa

Wani magidanci mai kimanin shekara 42 mai suna Ayuba Sunday da ke garin Gwadanye a Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa da ake zargi da sayar da ’ya’yansa ya shiga hannun jami’n Hukumar Sibil Difens bayan an kama shi kan zargin sayar da dansa mai shekara uku a kan Naira miliyan biyar. Da yake gabatar […]

An kama wanda ke sayar da ’ya’yansa a Nasarawa

Ayuba Sunday da xansa da ya so sayarwa

Wani magidanci mai kimanin shekara 42 mai suna Ayuba Sunday da ke garin Gwadanye a Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa da ake zargi da sayar da ’ya’yansa ya shiga hannun jami’n Hukumar Sibil Difens bayan an kama shi kan zargin sayar da dansa mai shekara uku a kan Naira miliyan biyar.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Lafiya, Kwamandan Hukumar Mohmoud Bala Fari ya ce, “Wannan laifi ne da ya fi na cin zarafin yara karami da aka saba yi. Wannan mutum da kuke gani a gabanku shi ne mahaifin wannan karamin yaro kuma shekararsa 42. Yana da mata biyar amma daga baya ya saki  daya saura hudu. Kuma yana da ’ya’ya 22 kafin ya sayar da ’yarsa ga wadansu matsafa a garin Owere babban birnin Jihar Imo kwanakin baya inda a yanzu haka muka hada kai da abokan aikinmu a jihar don kama wadanda suka sayi yarinyar a can,’ inji shi.

Ya ce wanda ake zargin yana yunkurin sake sayar da wannan karamin yaro ne da tsohuwar matarsa ta haifa a garin Lafiya kafin a kama shi. “Da muka samu labarin sirri cewa yana neman wanda zai sayar masa da yaron ne sai muka hada masa tarko, inda muka tura jami’anmu na sirri suka same shi cewa za su sayi yaron. Nan take ya amince zai sayar musu da shi inda suka shirya a kan Naira miliyan biyar. Da suka gama cinikin ne sai ya bukaci su turo masa kudin ta lambar asusunsa na banki. Sai jami’anmu suka ce ya zo da jaka da yaron za su jira shi a wani waje inda ya amince ya je wurin da buhun da zai zuba kudin da kuma yaron inda nan take suka kama shi,” inji shi.

Ya ce da aka zo da shi nan ya tambaye shi abin da ya sa ya yi yunkurin yin haka sai ya ce ya so ya yi haka ne don matsalar rashin kudi da yake fuskanta.

Da walilinmu ya tambayi wanda ake zargi da yunkurin sayar da dansa  ya bayyana cewa ya aikata haka ne don ya biya wasu bukatu da yake da su wadanda a cewarsa sun shafi iyalansa kasancewar yana da mata hudu ga ’ya’ya sama da 20 kuma babu wanda ke tallafa masa. Sai dai ya musanta zargin da ake masa cewa ya taba sayar da ’yarsa a Jihar Imo inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

Kwamandan ya kuma gabatar da wani magidanci mai shekara 45 mai suna Garba Wamba, wanda  ya ce sun kama shi ne bisa zargin yi wa yarinya mai shekara 10 da ke  garin Lafiya fyade. Ya ce bayan iyayenta sun lura jini na fitowa ta gabanta ne sai suka soma yi mata tambayoyi dangane da wanda ya aikata mata haka inda ta sanar da su. “A bincikenmu mun gano cewa wanda ake zargin wanda makwabcin su yarinyar ne ya rude ta ce da wasu kudi inda ta bi shi dakinsa ya yi mata fyade. Kuma da muka kama shi bai yi musu ba,” inji Kwamandan