An kama wanda suka yi wa mahaukaciya fyade a Anambra

Hukumar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama mutum biyu da ake zarginsu da yi wa wata mahaukaciya fyade a unguwar Ezi Umunya da ke Karamar Hukumar Oyi a jihar Anambra. Wanda ake zargin nasu da aikata laifin fyaden su ne: Okwuchukwu Anyanwu da Emeka Odoh, sun yi amfani da dama na rashin hankalin budurwar mai […]

An kama wanda suka yi wa mahaukaciya fyade a Anambra

Hukumar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama mutum biyu da ake zarginsu da yi wa wata mahaukaciya fyade a unguwar Ezi Umunya da ke Karamar Hukumar Oyi a jihar Anambra.

Wanda ake zargin nasu da aikata laifin fyaden su ne: Okwuchukwu Anyanwu da Emeka Odoh, sun yi amfani da dama na rashin hankalin budurwar mai shekara 23 wajen yin lalata da ita.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Anambra Haruna Mohammed, ya ce wadanda aka kaman bayan binciken su za a mika su gaban kotu, don yanke masu hukuncin da ya dace.