An kama wanda ya addabi mutane da satar shanu
Al’ummar garin Tankarau sun kama wani mai suna Zubairu Ibrahim dan asali garin danja da ke Jihar Katsina da suke zagin ya addabe su da sace musu shanu. Aminiya ta ziyarci gidan wanda ake zargin a kauyen Madaci da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, inda ta tarar da jama’a su yi cincirido suna […]

Al’ummar garin Tankarau sun kama wani mai suna Zubairu Ibrahim dan asali garin danja da ke Jihar Katsina da suke zagin ya addabe su da sace musu shanu.
Aminiya ta ziyarci gidan wanda ake zargin a kauyen Madaci da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, inda ta tarar da jama’a su yi cincirido suna ta fadin albarkacin bakinsu, wadansu suna cewa a kashe shi, wadansu na cewa kada a dauki doka a hannu.
Sarkin Fulanin Tukur-Tukur, Alhaji Shehu Jumare ya shaida wa wakilinmu cewa: “Allah Ya biya mana bukatarmu yau, kullum muna rokon Allah domin daga kaka zuwa yanzu an sace mana shanu sama da 50. Kullum muna rokon Allah a kai domin satar ta yi yawa yau a je nan, gobe a je can, wannan yaro (ya nuna wani ya ce) cikin watan jiya an sace masa shanu biyu mata, ni kai na an sace min shanu biyu amma Allah bai sa mun kama kowa ba, da mun biyo kafa mun zo wannan gida sai mu ga kafar ta bace sai mu hakura tunda dai ba mu ga inda aka shiga ba sai yau da Allah Ya kawo karshe.”
Alhaji Shehu Jumare ya ce, “A daren Sallah misalin karfe 3:00 na dare sai wanda ake zargin ya zo gida danmu mai suna Kadade Tambaya ya kwance masa shanu biyu mata ya kora su, sai muka bi sawu muna zuwa gida sai muka ga daga nan ba inda aka bi da shanun, don haka tunda dama muna zargin wannan gidan sai muka shiga muna shiga sai muka ga shanun a wani daki a daure ya kuma daure musu baki domin kada su yi kuka, daga nan sai muka sanar da ’yan sanda domin su yi bincike yanzu su muke jira.”
Duk da kokarin da Aminiya ta yi don daukar hoton wanda ake zargin ya ci tura, sai dai wanda ake zargin, Zubairu Ibrahim ya tabbatar wa Aminiya cewa shi ne ya saci shanun, kuma ya ce yana kai wa wani mutum ne a Kano, kuma ya ce yana haya ne a gidan da aka kama shi.
Ofishin ’yan sanda na dan Magaji ne ke bicike a kan lamarin kuma shugabansu, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, suna dada bincike a kai.
Sabon Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ya ce bai riga ya zauna ba sai makon gobe don haka bai san bayanin ba.