An kama wanda ya yi barazanar kashe ‘yar Majalisar Amurka Ilhan Omar
Jami’an tsaro a Amurka sun samu nasarar kama wanda ya yi barazanar zai kashe ’yar Majalisar Amurka Musulma wadda ita ce ta farko da ke daura dankwali a tarihin majalisar, wato Ilhan Omar a birnin New York. Alkalin yankin New York ya bayyana cewa an zargi Patrick Carlineo mazauni garin Addison da ke karkashin gundumar […]
Jami’an tsaro a Amurka sun samu nasarar kama wanda ya yi barazanar zai kashe ’yar Majalisar Amurka Musulma wadda ita ce ta farko da ke daura dankwali a tarihin majalisar, wato Ilhan Omar a birnin New York.
Alkalin yankin New York ya bayyana cewa an zargi Patrick Carlineo mazauni garin Addison da ke karkashin gundumar New York da barazanar zai kashe ’yar majalisa Ilhan Omar.
An bayyana zargin kisan kasancewar yadda Carlineo ya kira lamabar ofishin Ilham Omar inda yake cewa ma’aikatan ofishin, “Ku Omar ne kuke yi wa aiki, me ya sa kuke yi mata aiki, ’yar ta’addace, sai na harbe ta da harsashi.”
A yayin da Ilham Omar ta sanar wa Hukumar Bincike ta FBI, sai aka soma gudanar da kwakkwaran bincike a kan lamarin inda aka kama Carlineo daga baya.
Carlineo ya shaida wa Hukumar FBI cewa, “Ni dan kasa ne mai son Shugaba Donald Trump, ina kuma mai matukar kyamar Musulmi masu tsattsauran ra’ayi a cikin gwamnatinmu.”
An bayyana cewa harin bam da aka kai a wani otel da ke Los Angeles inda Ilham Omar ta sauka a lokacin da ta ziyarci birnin domin wani taro an yi haka ne domin kalubalantar rayuwarta kamar yadda kafar TRT ta ruwaito.