An kama wanda ya yi kokarin sayar da matarsa ga matsafa
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wani mutum mai suna Maimako Shepnang da yake zaune a kauyen Kwalla a karamar Hukumar kuan Pan, bisa zarginsa da kokarin sayar da matarsa ga matsafa kan Naira dubu 800.Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Jos, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato, Mista Nasiru […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wani mutum mai suna Maimako Shepnang da yake zaune a kauyen Kwalla a karamar Hukumar kuan Pan, bisa zarginsa da kokarin sayar da matarsa ga matsafa kan Naira dubu 800.
Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Jos, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato, Mista Nasiru Oki ya ce a ranar 30 ga Agustan da ya gabata, ’yan sanda a karamar Hukumar kuan Pan sun kama Maimako Shepnang bayan da suka
samu rahoton cewa, ya je ya sayar wa matsafa matarsa mai suna Agnes.
Ya ce da farko Maimako Shepnang ya karbi Naira dubu 400 daga wajen matsafan, daga nan sai ya dauke ta zuwa cikin daji da niyyar su je su saro itace. Bayan da suka shiga dajin ne sai wasu mutum biyu wadanda suka rufe fuskarsu suka zo suka same su, daga nan ne Maimako Shepnang ya mika matarsa ga mutanen.
Kwamishinan ya ce bayan da Maimako Shepnang ya tafi sai matsafan suka tambayi matar ko ta taba yin aure? Sai Agnes ta ce ai wancan mutumin da ya kawo ta mijinta ne. Da suka ji wannan bayani, sai suka sake ta, suka ce ta gudu domin su suna bukatar
budurwa ce a tsafin da suke son su yi.
Kwamishinan ya ce daya daga cikin matsafan da aka kama ya tabbatar wa ’yan sanda wannan zargi da ake yi masu, kuma ’yan sanda suna ci gaba da bincike.
Da yake zantawa da manema labarai Maimako Shepnang ya ce talauci ne ya sanya shi aikata wannan mummunan al’amari. Ya ce, “Muna rayuwa a cikin talauci, ba ni da abin yi. Don haka na ce da matar tawa ta biyo ni zuwa daji mu je saro itace. Da ma mun riga mun shirya da mutanen cewa na kawo musu budurwa don su yi tsafi, za su ba ni Naira dubu 800.”
Ya ce sun fara ba shi Naira dubu 400 da alkawarin za su cika masa Naira dubu 400, “Don haka bayan da muka shiga cikin dajin da matata sai na mika musu ita. Abin mamaki bayan na koma gida sai kawai na ga matar tawa ta zo da ’yan sanda suka kama ni.”
Daga Hussaini Isah, Jos
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wani mutum mai suna Maimako Shepnang da yake zaune a qauyen Kwalla a Qaramar Hukumar Quan Pan, bisa zarginsa da qoqarin sayar da matarsa ga matsafa kan Naira dubu 800.
Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Jos, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato, Mista Nasiru Oki ya ce a ranar 30 ga Agustan da ya gabata, ’yan sanda a Qaramar Hukumar Quan Pan sun kama Maimako Shepnang bayan da suka
samu rahoton cewa, ya je ya sayar wa matsafa matarsa mai suna Agnes.
Ya ce da farko Maimako Shepnang ya karvi Naira dubu 400 daga wajen matsafan, daga nan sai ya xauke ta zuwa cikin daji da niyyar su je su saro itace. Bayan da suka shiga dajin ne sai wasu mutum biyu waxanda suka rufe fuskarsu suka zo suka same su, daga nan ne Maimako Shepnang ya miqa matarsa ga mutanen.
Kwamishinan ya ce bayan da Maimako Shepnang ya tafi sai matsafan suka tambayi matar ko ta tava yin aure? Sai Agnes ta ce ai wancan mutumin da ya kawo ta mijinta ne. Da suka ji wannan bayani, sai suka sake ta, suka ce ta gudu domin su suna buqatar
budurwa ce a tsafin da suke son su yi.
Kwamishinan ya ce xaya daga cikin matsafan da aka kama ya tabbatar wa ’yan sanda wannan zargi da ake yi masu, kuma ’yan sanda suna ci gaba da bincike.
Da yake zantawa da manema labarai Maimako Shepnang ya ce talauci ne ya sanya shi aikata wannan mummunan al’amari. Ya ce, “Muna rayuwa a cikin talauci, ba ni da abin yi. Don haka na ce da matar tawa ta biyo ni zuwa daji mu je saro itace. Da ma mun riga mun shirya da mutanen cewa na kawo musu budurwa don su yi tsafi, za su ba ni Naira dubu 800.”
Ya ce sun fara ba shi Naira dubu 400 da alqawarin za su cika masa Naira dubu 400, “Don haka bayan da muka shiga cikin dajin da matata sai na miqa musu ita. Abin mamaki bayan na koma gida sai kawai na ga matar tawa ta zo da ’yan sanda suka kama ni.”