An kama wanda ya yi wa mahaifinsa dukan mutuwa a Ondo

Lamarin mai ban tausayi ya faru ne a ranar 28 ga Mayu, 2026, lokacin da wanda ake zargin yake takaddama da mahaifinsa, hakan ya rikide zuwa dambe da dukan juna.

An kama wanda ya yi wa mahaifinsa dukan mutuwa a Ondo

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta kama wani mutum mai shekara 38, Nsikak Kingsley saboda zargin dukan mahaifinsa.

Mahaifin mai suna Adone Peter, mai shekara 65, har lahira biyo bayan wani rikici na ba-ta-kashi da ya faru a yankin Oda, da ke Ƙaramar Hukumar Akure ta Kudu a jihar.

​Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar (PPRO), DSP Abayomi Jimoh, ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, Felix Ohagwu.

​A cewar hukumar ’yan sanda, lamarin mai ban tausayi ya faru ne a ranar 28 ga Mayu, 2026, lokacin da wanda ake zargin yake takaddama da mahaifinsa, hakan ya rikide zuwa dambe da dukan juna.

​Yayin rikicin, an bayyana cewa mahaifin ya sami munanan raunuka, musamman a kansa, inda aka yi gaggawar kai shi wata cibiyar lafiya domin yi masa magani. Sai dai daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsa yayin da yake karɓar magani.

‘Yan sandan sun bayyana cewa, Daniel Moses, wani ɗan mamacin kuma ɗan’uwa ga wanda ake zargin, ne ya kai rahoton lamarin, lamarin da ya sa jami’an binciken sirri suka bazama domin gudanar da bincike.

​”Sakamakon hanzarta ɗaukar mataki kan rahoton, jami’an ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin kuma aka tsare shi domin yi masa tambayoyi,” in ji shi.

An ajiye gawar mamacin a ɗakin ijiye gawa na asibiti domin gudanar da binciken gano musabbabin mutuwarsa , yayin da aka tura maganar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin ci gaba da bincike.

​Wanda ake zargin yana tsare a hannun ’yan sanda kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala bincike.