An kama wanda yake yi wa rayuwar Atiku da iyalinsa barazana
Hukumar ‘yan sanda ta bayyana nasarar kama wani mutum da ya yi barazanar kashe tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar tare da iyalansa. Mutumin da aka kama mai su na Augustus Akpan ne dan shekara 43, a Lagos, da jami’an ‘yan sandan suka bankado inda ya ke, ta hanyar amfani da na’urar gane duk inda […]
Hukumar ‘yan sanda ta bayyana nasarar kama wani mutum da ya yi barazanar kashe tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar tare da iyalansa.
Mutumin da aka kama mai su na Augustus Akpan ne dan shekara 43, a Lagos, da jami’an ‘yan sandan suka bankado inda ya ke, ta hanyar amfani da na’urar gane duk inda wata wayar tafi da gidanka ta ke.
Akpan na amfani da wayar sata wajen aika sakonnin barazana ga Atiku da iyalansa, mai barazanar ya kware a harshen turanci da Ibibio da Rasha da kuma na kasar Portugal a jiya Laraba.
Wayar tafi da gidanka da aka kama Akpan da ita, ita ce ya ke amfani wajen tura wa Atiku sakonnin tes na yi masa barazana shi da iyalansa.
A cikin makon jiya ne Atiku ya kai korafin ga hukumar ‘yan sandan Najeriya cewa, akwai masu yi wa ran sa da na iyalan sa barazana. Sai dai Akpan ya shaida wa ‘yan sanda cewa, barazanar da ya yi wa Atiku ta tada-kura ce kawai da kuma burga, ba don siyasa ba.
Jami’in yada labarai na ‘yan sandan birnin tarayya Jimoh Moshood, ya ce Akpan ya sha yi wa wandanda suka rike mukamai da sauran jama’a barazana ya na damfarar su makudan kudade, nan bada dadewa ba za a gurfanar shi a kotu don yanke masa hukunci da ya dace.