An kama wani babban kwamandan Boko Haram a Chadi
Wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Fanay da ake wa lakabi da Mahamat Moustapha da Baana Fanay, sun shiga hannu a Jamhuriyyar Chadi, inda kama shi ya jawo kama wasu jigogin kungiyar da dama. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Babban Mai gabatar da kara na kasar Chadi, Alghassim Khamis, yana […]
Wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Fanay da ake wa lakabi da Mahamat Moustapha da Baana Fanay, sun shiga hannu a Jamhuriyyar Chadi, inda kama shi ya jawo kama wasu jigogin kungiyar da dama.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Babban Mai gabatar da kara na kasar Chadi, Alghassim Khamis, yana cewa Fanay ne yake shirya yadda ake safarar makami zuwa Najeriya da Kamaru da Chadi kuma an kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Jammaina da ke kasar Chadi.
Ya kara da cewa, an kama shi tare da wasu ’yan ta’adda biyu kuma shi ne ke da alhakin sayo makamai da daukar mayakan Boko Haram.
Bincike a gidan wanda ake zargin ya jawo kama wasu nau’o’in makamai da takardun da Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya rubuta da Larabci kan yadda za a dauki mayakan kungiyar.
Ya ce wannan kamu ya jagoranci masu bincike zuwa ga gano wasu ’yan ta’adda bakwai da suke boye a wani gida a Diguel da ke wajen garin Dinguessou a kusa da Jammaina.
Khamis ya ce wani mutum da ake da yakinin shi ne mai samar wa kungiyar kudi ya shiga hannu kuma ana gudanar da bincike a kansa.
Y ace sakamakon binciken zai taimaka wajen murkushe kungiyar Boko Haram a kasar.
Bayan kai miygun hare-haren da suka hallaka mutum 38 tare da raunata 100 a Jammaina a ranar 15 ga Yuni, jami’an tsaro a kasar Chadi sun kama mutum 74 da ake zargi da hannu a hare-haren.